Wasu da ake zargin ‘yanta’adda ne sun kashe manoma 11 a hare-hare biyu daban-daban da suka kai a arewa maso gabashin Nijeriya a karshen mako.
A ranar Asabar, maharan sun tattara manoma bakwai a ƙauyen Kuwawu da ke jihar Borno sannan suka yi musu yankar rago, kamar yadda ‘yan bijilanti na yankin suka shaida wa AFP.
Sun ɗora alhakin harin kan mayakan Daesh-WAP, wata ƙungiya wadda ta ɓalle daga ƙungiyar Boko Haram da ke da sansani a Borno.
“Dukkan manoman bakwai mayakan Daesh-WAP ne suka yanka su, kuma an gano gawawwakinsu tare da binne su jiya,” in ji ɗan bijilanti Babakura Kolo ga AFP.
A cewar wani ɗan bijilanti, Ibrahim Liman, manoman sun fito ne daga garin Monguno mai sansanin sojoji domin su shirya gonakinsu don shuka amfanin gona.
Tun da farko a ranar, an kuma kashe wasu manoma huɗu a gonakinsu da ke wajen Kross Kauwa a yankin Tafkin Chadi, kimanin kilomita 50 daga Monguno.
Wani ɗan bijilanti mai suna Musa Ari ya ɗora alhakin kashe su kan mayaƙan Daesh-WAP.
An san Daesh-WAP da Boko Haram da kai hare-hare kan manoma, masu sare itatuwa, makiyaya da ‘yan gwangwan, saboda zarginsu da yi wa sojojin Nijeriya da kungiyoyin bijilanti leƙen asiri.
A makon da ya gabata, an kashe manoma 17 tare da raunata wasu biyar a Jihar Zamfara, a wani hari da jami’ai da mazauna yankin suka ɗora alhakinsa kan ƙungiyoyin masu aikata laifuka.
A halin da ake ciki, Asusun Bayar da Lamuni na Duniya ya yi kira ga gwamnati da ta ƙara kare manoma da makiyaya.
Arewacin Nijeriya ne ke samar da kusan kashi 70 cikin 100 na hatsin da ake nomawa a ƙasar, wanda ake amfani da shi a gida tare da fitar da wani ɓangare zuwa ƙasashe maƙwabta na Yammacin Afirka.















