5 Sep, 2026

Nijar na zargin Faransa da tunzura sojojin da suka yi yunkurin tawayen da aka dakile

Gwamnatin Nijar ta gudanar da taron Majalisar Ministoci a ranar Jumma’a, wanda shi ne karo na farko tun bayan yunƙurin tawayen da wasu sojoji suka yi a ƙasar inda gwamnatin ta bayyana waɗanda take zargi suna da hannu a shirin tawayen.

4 Sep, 2026

Tallafin ƙasashen waje da harin jiragen sama marasa matuƙa sun ƙara tsananta yaƙin Sudan – MDD

An kashe mutane fiye da 1,000 a hare-haren jiragen sama marasa matuƙa a cikin watanni biyar na farko na 2026, a cewar binciken rahoton da tawagar MDD ta fitar, inda ta zargi ɓangarorin biyu da aikata manyan laifuka na take haƙƙin ɗan adam.

b1095892 fb50 4221 ab7d 6806049cc454 1785523855513

3 Sep, 2026

Babban hafsan sojin Sudan Burhan na rangaɗi game da shirin yaƙi a fagen yaƙin Blue Nile

Ziyarar Abdel Fattah al-Burhan na zuwa ne a cikin ƙarin arangama tsakanin soji da RSF a jihar Blue Nile.

588e2c4c 7be4 44dc 8437 47543d4d84b6 1788416901227

2 Sep, 2026

Dubban mutane sun yi zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga sojin Nijar bayan dakile yunƙurin tawaye

Zanga-zangar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan magoya bayan gwamnatin sojin sun dakile yunƙurin tayar da zaune tsaye.

87b9e8e4 1b89 436e a00e 10e12d32d51f 1788354660188

2 Sep, 2026

Shugaban ƙungiyar Tarayyar Afirka ya yi Allah wadai da boren da aka yi a Nijar

Boren ya yi sanadin mutuwar mutane biyar, a cewar rahotannin kafofin watsa labarai.

5c9a0c3d d20d 4b03 a054 3d6e9931c4f3 1778681756795

31 Aug, 2026

Tebboune ya sake bayyana goyon bayan Aljeriya ga Nijar yayin da ake fuskantar barazanar tsaro

Jiragen sojojin Aljeriya huɗu sun isa Yamai yayin da sojojin Nijar suka yi ƙoƙarin ƙwato iko wani wuri mai muhimmanci da aka kai wa farmaki a hare-haren da suka faru a babban birnin ƙasar.

c7296db6 7ee4 49e0 b214 c93ca7169b09 1788189896791

31 Aug, 2026

Mayaƙa 200 sun fice daga RSF ta Sudan inda suka sauya sheƙa zuwa rundunar sojin ƙasar

Mayaƙan ƙarƙashin jagorancin Abu Bakr Hamouda Dahloop sun ce sun fahimci kuskuren da suka tafka na shiga ƙungiyar RSF inda suka tabbatar da komawa ɓangaren sojin ƙasar tare da alƙwarin yaƙi don kawar da RSF.

6f626551 1f2e 4efd a19a c1c9e2389300 1788170537943

31 Aug, 2026

Algeria ta aika jiragen yaƙi huɗu zuwa Jamhuriyar Niger bayan tashin hankali a Niamey

Jiragen yaƙi na sintiri sun sauka a filin jirgin sama na Yamai, tare da rakiyar jirgin ƙara wa jirage mai, a cewar Ma’aikatar Tsaro ta Jamuhuriya Nijar.

6b15b5cb 1a13 4915 8674 441eecc2de96 1788121970026 main

30 Aug, 2026

Boren soji a Yamai: AES ta jaddada goyon bayanta ga Nijar, ta yaba wa martanin dakarun tsaro

An shafe sa’o’i ana jin harbe-harbe masu ƙarfi cikin daren Asabar zuwa safiyar Lahadi a Yamai babban birnin ƙasar yayin da wasu sojoji suka yi boren da ma’aikatar tsaron ƙasar ta ce dakarun gwamnati sun samu sun daƙile shi.

e4ae7795 3eff 4210 a5e8 82a195ea724c 1788077482423 main

29 Aug, 2026

An ji karar harbe-harben bindiga a kusa da sansanin soji da kuma fadar shugaban kasa a Nijar

Jama’a da dama a kafafen sada zumunta waɗanda ke zaune a Nijar sun kuma ruwaito cewa an ji harbe-harbe da fashe-fashe a cikin birnin, musamman a yankin gwamnati inda fadar shugaban ƙasa da gidan talabijin na ƙasa suke.

bf69baa4 b675 4011 b0ea 99ed60b54ac3 1787985646784 main
Loading...