Ƙungiyar yarjejeniyar tsaro ta Makka ta tattauna kan yin taron gaggawa don tallafa wa Saudiyya

Ministocin harkokin waje na kasashe uku da suka kafa kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Makka sun tattauna kan shirye-shiryen taron manyan hafsoshin soji, wanda zai yi nazari kan hanyoyin tallafawa Saudiyya bisa alkawuran da ke cikin yarjejeniyar.
25 Sep, 2026
Iran ta yi tayin sake buɗe Mashigar Hormuz cikin kwanaki bakwai idan Amurka ta sassauta matsin lamba

Kamfanin dillanacin labarai na Turkiyya, Anadolu ya ce bai iya tabbatar da sahihancin wannan batu ba da kansa.
22 Sep, 2026
Birtaniya za ta bai wa Saudiyya ‘kariyar’ soji don daƙile hare-haren ‘yan Houthi

Birtaniya ta tura jirgin ba da mai a sama domin bai wa jiragen saman Saudiyya damar shan mai yayin da hare-haren ‘yan Houthi ke barazana ga safarar jiragen ruwa na masarautar da ma yankin baki ɗaya.
22 Sep, 2026
Amurka ta ce za a dakatar da zirga-zirgar dukkan kamfanonin jiragen saman Iran a duniya daga Laraba

Ya ce filayen jiragen saman kasa da kasa da ke kula da jiragen Iran za su fuskanci cikakken katsewa daga tsarin hada-hadar bankunan Amurka.
21 Sep, 2026

Qatar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran

Yaƙin Amurka da Iran ya laƙume $150B na tattalin arzikin ƙasashen Larabawa a cikin wata guda: MDD

Amurka ta hana shugaban Falasɗinawa bizar halartar Babban Taron MDD a karo na biyu

Kungiyar OIC ta yi Allah wadai da hare-haren ‘yan Houthi a Makka da yankin Madina

Yaƙin Yemen ya raba fiye da mutum 100,000 da muhallansu — Majalisar Ɗinkin Duniya
15 Sep, 2026
Iran ta ba da umarni a yi shirin yaƙi da tsagaita wuta da yanayin bayan yaƙi ga dukkan ƙasar
Umarnin ya yi kira ga daukar matakai daga hukumomi da jama’ar kasa duba ga ko yakin zai ci gaba, zai tsahirta ko kuma ya zo karshe ne baki daya.

15 Sep, 2026
Hukumar sa ido kan Pentagon ta ce yaƙin Iran ya jawo ƙarancin makamai ‘masu mahimmanci’
Rundunar sojin Amurka na fuskantar ƙarancin makamai masu mahimmanci yayin da watanni na yaƙi da Iran suka nuna matsalolin samar da makamai.

12 Sep, 2026
Saudiyya ta ce wasu jirage marasa matuƙa da aka aika daga Iraƙi sun kai hari kan wani bututun mai
Saudiyya ta ce jiragen sama marasa matuƙa da aka aika daga Iraƙi sun kai hari kan bututun da ke jigilar mai daga Gabashin Saudiyya zuwa Yammaci, lamarin da ya kai ga rufe bututun.

11 Sep, 2026
Amurka ta yi biris da kiran Saudiyya na kai wa Houthi hari, ta ce za ta ba da taimakon bayanan sirri
Washington na fifita tauna tsakuwa aya ta ji tsoro a yakin Iran, yayin da ta aika da shugaban CENTCOM zuwa Riyadh don tattaunawa.

10 Sep, 2026
Isra’ila ta sake jaddada barazanar kai hari wuraren makamashin Iran
“Duk wani hari kan Isra’ila, ko da wane dalili kuma daga ko ina aka kai shi, za a mayar da martani mai ƙarfi.”

9 Sep, 2026
Iran ta kai hari kan sansanin sojoji da jiragen yaƙin Amurka da ke Jordan
Amman ta ce ta kakkaɓo makamai masu linzami 18 na Iran, yayin da biyu suka sauka a wuraren da babu jama’a ba tare da sun yi sanadiyyar mutuwar fararen-hula ba.

8 Sep, 2026
Ministocin Larabawa sun yi watsi da shirin korar Falasdinawa, suna neman a kare Gaza
Sun yi gargaɗin cewa duk wani tilasta wa Falasɗinawa barin gidajensu zai zama tsarkake ƙabila kuma ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.

8 Sep, 2026
Iran ta yi gargadin cewa matsin lambar Amurka na iya sakawa a hana jiragen ruwa shiga tekun Gulf
Wani babban jami’in tsaron Iran ya ce, Tehran ta “sauya dabarunta” na soji kuma yanzu a shirye take ta mayar da martani mai tsauri kan jiragen ruwan yaƙi na Amurka da sansanonin sojinta a yankin.

7 Sep, 2026
Masu aikin Umrah biyu sun rasu, 25 sun jikkata bayan bas ɗauke da ‘yan ƙasar Masar ta yi hatsari
Ma’aikatar Harkokin Wajen Masar ta ce bas ɗin, wadda ke ɗauke da mahajjata ’yan ƙasar Masar 47, tana kan hanya daga Madina zuwa Makkah lokacin da hatsarin ya afku.

4 Sep, 2026
Ben-Givir na Isra’ila ya gabatar da shirinsa na korar Falasɗinawa 1.8m daga Gaza a shekara bakwai
Rahoton ya ce shirin na da burin korar Falasɗinawa 250,000 a shekarar farko, miliyan 1.11 cikin shekaru uku, sannan kusan miliyan 1.86 cikin shekaru bakwai.



