Iran da Oman sun amince kan gudanar da hanyar ratsawar jiragen ruwa ta Mashigar Hormuz kuma suna shirin cim ma yarjejeniyar ƙarshe kan shirye-shiryen gudanar da hanyar tare, in ji ma’aikatar harkokin wajen Tehran.
“An amince da tsarin yanayin ƙasa na hanyar da ɓangarorin biyu suka tsara, kuma idan wasu ɓangarorin na uku ba su kawo cikas ga tsarin ba, sanarwar haɗin gwiwa ta ƙasashen biyu, wadda ta ƙunshi manyan abubuwan da aka yi la’akari da su da kuma abubuwan da aka cim ma, za a shigar cikin matakin ƙarshe na bita da tsarawa,” kamar yadda mai magana da yawun Tehran kana ministan harkokin wajen ƙasar Esmaeil Baqaei ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na IRNA a ranar Laraba.
Baqaei ya shaida wa manema labarai cewa ana ci gaba da tattaunawa da Oman, kuma ko da an cim ma yarjejeniyar ta ƙarshe, hakan ba ya nufin cewa mashiginar za ta kasance cikin tsaro ga dukkan jiragen ruwa da ke wucewa ta hanyar ba, a cewar rahoton.
“Abubuwan da suka sanya hanyar mashigar Hormuz ta kasance cikin rashin tsaro har yanzu suna nan a ɓangaren Amurka, musamman shingen jiragen ruwa da sauran ayyuka masu barazana ga Iran da muradunta,” in ji shi.
“Hukumomin da suka cancanta a ƙasarmu sun sake duba shawarar daga mahangar fasaha da shari’a da tsaro da kuma muhalli,” in ji Baqaei.
Ya bayyana tattaunawar a matsayin wadda aka yi amfani da “ƙwarewa” kuma “mai muhimmaci”, ya ƙara da cewa ɓangarorin biyu sun amince kan daidaita yanayin hanyar da aka tsara.
Tun a watan Fabrairu Iran ta shiga rikici da Amurka, bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Tehran.
A ɓangare guda, Iran ta mayar da martani da hare-haren jiragen sama marasa matuka da makamai masu linzami kan ƙasashen yankin Gulf da ke ɗauke da kadarorin Amurka.
Amurka da Iran sun amince da tsagaita wuta a watan Afrilu sannan daga baya suka sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna da Pakistan ta shiga tsakani a watan Yuni da nufin kawo ƙarshen rikicin soja da cim ma yarjejeniyar zaman lafiya mai ɗorewa.
Sai dai, yarjejeniyar ta ruguje a watan da ya wuce, inda ɓangarorin biyu suka yi musayar hare-hare na kusan makonni biyu kafin Trump ya dakatar da luguden a wani yanayi na zato ba tsammani a yayin da ake samun rahotannin tattaunawa don warware rikicin.
Kafin soma yaƙin, ana fitar da kusan kashi ɗaya bisa biyar na man fetur da iskar gas da duniya ke amfani ta hanyar Hormuz, kana an yi ta samun hauhawar farashi akai-akai tun barkewar takaddama kan hanyar ruwa, lamarin da ya haifar da matsin lamba ga Washington kan tattalin arziki da siyasa.















