Jami’an Rundunar Operation Damissa ta Nijar sun lalata wasu wurare da ake zargin mayaƙan ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai ne ke amfani da su a matsayin maɓoya a wani samame da suka kai yankin Dosso, a cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Nijar, ANP a ranar Talata.
Kazalika kafar ta ruwaito cewa aikin ya gudana ne a ranar 8 ga watan Satumba a yankin Kaberi, inda jami’an tsaron suka gano wasu wurare da ke cikin dazuzzuka.
“An lalata bukkoki da matsugunai da dama da ake zargin ana amfani da su wajen ɓoye mayaƙa da kuma tarurrukan ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai,” in ji Kwamandan rundunar.
Jami’an tsaron sun kuma ƙwato bindigar AK-47 ɗauke da harsasai a cikin ta da kuma wayar salula, waɗanda hukumomin suka ce an bar su ne bayan waaɗnda ake zargin sun tsere.
A hanyar Faska-Koukoki, jami’an tsaro sun tare wasu babura uku, amma mutanen da ke kansu sun tsere bayan sun hango jami’an tsaron. Daga bisani, an lalata baburan, a cewar rahoton.
Ana ci gaba da gudanar da ayyukan tsaro a wasu yankuna
Abin da ya faru a Dosso na daga cikin jerin ayyukan tsaro da ake gudanarwa a sassan Nijar domin daƙile ayyukan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
A yankin Diffa da ke gabashin ƙasar, jami’an tsaro na rundunar Operation Naléwa Dolé sun ce sun kama mutane biyu da ake zargin mambobin Boko Haram ne a Bosso a ranar 3 ga Satumba.
Hukumomin sun kuma ce, an kama wasu mutane biyu da ake zargin ‘yan leƙen asiri ne a ranar 4 ga Satumba, yayin da a ranar 7 ga Satumba aka kama wasu mutane uku da ake zargin suna kera na’urorin fashewa, ciki har da mata biyu, a Bosso.
Rahoton ya kuma ce, a ranar 8 ga Satumba, jami’an tsaro sun ƙwace wasu yaduna masu yawa na kayan sojoji, wanda ake zargin an shirya kai wa ‘yan Boko Haram ne.
“Wasu tsoffin mambobin Boko Haram biyu sun miƙa wuya ga jami’an tsaro a Bosso,” a cewar rahoton Cibiyar Kula da Ayyukan Haɗin Gwiwa (CICO) da ANP ta rawaito.
Haka kuma a wani samame da aka gudanar a yankin N’Gagala-Gonan Sarki, jami’an tsaro sun ce sun gano tare da lalata wasu wuraren da ake zargin ana ɓoye makamai da kayayyakin tallafa wa mayaƙa.
Waɗannan ayyukan na zuwa ne yayin da Nijar ke ci gaba da yaƙi da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a sassa daban-daban na ƙasar.















