Turkiyya ta sanar da sabon cikakken shirin aiwatar da manufofi domin zama cibiyar fasahar ƙirƙirarriyar basira (AI) ta duniya, ta hanyar cin gashin kanta ta hanyar fasaha da kuma samar da hanyoyin fasaha da za su sauƙaƙa al’amura a ta ɓangarori da dama na ƙasar.
Shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan ya sanya hannu kan takardar umarnin da ya shafi Shirin Aiwatar da Manufofin fasar AI ta Turkiyya na 2026–2030, sannan aka wallafa shi a cikin Mujjalar Ƙasa a ranar Talata.
Ma’aikatar Masana’antu da Fasaha ce ta tsara sabon tsarin da zai sabunta manufofin ƙasar daidai da tsarin ƙasar na samun cikakken ‘yanci ta fuskar fasaha da kuma samun sauyi mai ɗorewa a fannin dijital.
Gwamnati ta tsara tsarin ne bisa manyan matakai guda huɗu, waɗanda suka haɗa da wayar da kai, amfani, samarwa da kuma gudanarwa, domin gina ingantaccen tsarin AI mai aminci.
Wayar da kai da ƙwarewa
Shirin na da nufin bai wa ’yan ƙasa miliyan biyar a larduna 81 horon sanin makamar amfani da AI cikin shekaru biyu.
Hukumomi sun kuma ƙaddamar da wani shirin ƙasa na haɓaka ƙwarewa, wanda zai horas da ƙwararru 10,000 masu babban matakin ƙwarewa da kuma ƙwararrun aikace-aikacen AI 100,000.
Jami’ai sun shirya samar da aƙalla bayanan jama’a 2,000, tare da kafa tsarin doka da ɗabi’a domin kare haƙƙin masu amfani.
Samar da ababen more rayuwa
Turkiyya ta sanya wa kanta burin ƙara ƙarfin wutar da ake amfani da ita a ɓangaren sarrafa bayanai da ke cikin cibiyoyin adana bayanai zuwa gigawatt ɗaya nan da shekarar 2030.
Gwamnati ta ware awannin amfani da GPU miliyan 20 ga masu bincike, sabbin kamfanoni da ƙananan ’yan kasuwa, domin sauƙaƙa musu samun damar amfani da albarkatun sarrafa bayanai.
Shirin ya tilasta wa hukumomin gwamnati ware aƙalla kashi 2 cikin 100 na kasafin kuɗaɗen jarinsu domin ayyukan AI.
An kuma ƙaddamar da shirye-shiryen gwaji a wasu muhimman fannoni, musamman kiwon lafiya, makamashi da masana’antun zamani masu amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira.
Gwamnatin ta kuma yanke shawarar kafa yankunan bunƙasa AI a harabar jami’o’i, inda ake da sauƙin samun makamashi da sauran ababen more rayuwa.
Bugu da ƙari, jami’ai sun ƙirƙiri asusun binciken AI, tare da wani asusun bunƙasa kamfanoni, domin samar da kuɗin gudanar da ayyukan cikin gida.
Tsarin ya ƙarfafa masu haɓaka fasaha da su samar da kuma fitar da samfuran harshe na Turkiyya na musamman ga fannoni daban-daban, da kuma na’urorin mutum-mutumi masu iya gudanar da ayyuka a zahiri.
Jagorancin diflomasiyya a yankin
Turkiyya na da burin jawo aƙalla dala biliyan 10 na jarin kamfanoni masu zaman kansu da za a zuba a fannin AI da cibiyoyin adana bayanai.
Ƙasar ta kuma shirya taka rawa sosai a matakai na ƙasa da ƙasa kamar OECD, G20 da Majalisar Ɗinkin Duniya.
Ƙoƙarin haɗin gwiwar yankin ya haɗa da samar da babban samfurin harshe na bai ɗaya ga harsunan Turkawa, tare da gudanar da gwaje-gwajen tsarin dokoki aƙalla fannoni biyar da aka ware a matsayin masu muhimmanci.
Ministan Masana’antu da Fasaha, Mehmet Fatih Kacir, ya bayyana cewa AI na wakiltar wani sabon muhimmin abu da zai ƙayyade bunƙasar tattalin arziki da kuma ’yancin kan iyakokin ƙasa.
“Turkiyya ta yanke shawarar zama jagora maimakon kallon wannan sauyi na duniya daga gefe,” in ji ministan a ranar Talata.
Ya ce ƙasar na da burin gina wani tsari da zai samar da amintattun kayayyakin fasaha bisa nata ƙa’idoji, tare da faɗaɗa hanyoyin magance matsaloli zuwa fannoni masu muhimmanci.
Ministan ya ƙara da cewa Turkiyya na shirin amfani da waɗannan damammaki zuwa matakin da ya fi dacewa, domin jin daɗin al’umma da kuma amfanin bil’adama baki ɗaya.















