Girgizar ƙasa mai maki 5 ta girgiza gabashin Turkiyya

Girgizar ƙasar ta afka wa gundumar Battalgazi a wani wuri mai zurfi na kilomita 15.59, in ji hukumar bada agajin gaggawa ta Turkiyya.

Newstimehub

Newstimehub

18 Jul, 2026

2c9424f3 6839 4ca1 8c10 aeeb998f8d61 1784366805822

Wata girgizar ƙasa ma mai ƙarfin maki 5.0 ta afka wa lardin gabashin Turkiyya na Malatya a cikin sanyin safiyar ranar Asabar, in ji hukumar ba da again gaggawa ta Turkiyya (AFAD).

Girgizar ƙasar ta auku ne da misalin ƙarfe 6.20 na safiya na yankin (ƙarfe 03:20 agogon GMT), inda cibiyarta ta kasance a gundumar Battalgazi a wani wuri mai zurfin kilomita 15.59 (mil 9.69 ), in ji AFAD .

An ji motsin ƙasa a larduna masu maƙwabtaka da suka haɗa da Elazig da Adiyaman da Tunceli da kuma Sanliurfa.

AFAD ta ce babu wani rahoto na lalata abubuwa ko kuma mace-mace nan-take biyo bayan girgizar ƙasar.

Murat Kurum, ministan muhalli da girman birane da sauyin yanayi, shi ma ya bayanna a shafin sada zumuntan Turkiyya NSosyal cewa: “Biyo bayan girgizar ƙasar da aka yi a Battalgazi, ba a samu wani abu mai muni ba kawo yanzu, amma muna nazari kan dukkan rahotanni .”