Rundunar sojin Nijeriya ‘ta kashe ‘yanta’addan Boko Haram da ISWAP fiye da 1000 a shekara ɗaya’

Dakarun sojin sun kuma kwato harsasai fiye da 24,000, tare da lalata bama-bamai da aka ƙera su a gida, wato IED, 295. Ya ce an kama mutane 758 da ake zargi da taimakawa ‘yan ta’adda wajen safarar makamai da sauran kayan aiki.
16 Sep, 2026
Samun ɗa namiji magaji ba ya gabana. Ba na jin ɗa namji zai yi fiye da abin da ‘ya’yana mata uku suk

Dangote, wanda yake da ’ya’ya mata uku, ya ƙara da cewa bai yi imanin samun ɗa namiji zai haifar da sakamako mafi kyau fiye da abin da ’ya’yansa mata ukun suka cimma ba.
15 Sep, 2026
Rundunar ‘yansandan Nijeriya ta yi gargaɗi game da yiwuwar kai hare-hare makarantu da wuraren ibada

Rundunar ta umarci kwamishinonin ’yansanda da sauran sassan tsaro da su kara sa ido da sintiri da kuma binciken ababen hawa da mutane, tare da karfafa matakan tsaro a wuraren da ake ganin za su iya zama barazana na harin.
15 Sep, 2026
Ana zargin ‘yanta’adda da kashe aƙalla mutum 13 a wasu hare-hare a Jihar Filato ta Nijeriya

Hare-haren sun faru ne a daren Lahadi, inda aka kashe fasinjoji tara da ke tafiya zuwa Jos bayan wasu da ake zargin ’yanta’adda ne sun buɗe wa motarsu wuta a al’ummar Dungus da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu.
14 Sep, 2026

Matatar Dangote ta sayar da hannayen-jarin fiye da naira biliyan 10 mintuna kaɗan bayan ƙaddamarwa

‘Yansandan Nijeriya sun kama mutum 262, sun kuma ceto 27 da aka yi garkuwa da su

An sace malamai shida da suka je taron addu’ar APC a Zamfara

Gwamnatin Nijeriya ta yi Allah wadai da kisan ‘yan ƙasarta biyu a Afirka ta Kudu

Majalisar Dokokin Nijeriya ta dakatar da ziyarar aiki zuwa Afirka ta Kudu
11 Sep, 2026
Mutum 511 sun kamu da cutar mashaƙo a Jihar Yobe a Nijeriya
Ya bayyana cewa ɓullar cutar ta shafi ƙananan hukumomi 12 ne a jihar, yana mai ƙarawa da cewa shiri ya yi nisa don ƙaddamar da riga kafi kan cutar a waɗannan yankunan.

10 Sep, 2026
Amurka ta aika sabbin kayayyakin soji Nijeriya
An kwashe kayan aikin zuwa Nijeriya ne ta jirgin saman sojin Amurka kirar C-17 Globemaster III, ƙarƙashin tsarin sayar da kayan aikin soji na ƙasashen waje tsakanin Washington da Abuja.

10 Sep, 2026
Jakadan Nijeriya ya ziyarci ’yan kasar 198 da ke gidan yari a Indiya
Jakadan Nijeriya a Indiya, Ambasada Saidu Muhammad ya gana da ’yan Nijeriya 198 da ke tsare a lokacin ziyararsa zuwa kurkuku daban-daban a faɗin Indiya.

10 Sep, 2026
‘Yansandan Nijeriya sun kama mutum biyu kan zargin kashe Danshagamu a Kano
Sanarwar ta ce ana gudanar da bincike kan lamarin kuma za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala binciken.

9 Sep, 2026
Nijeriya ta naɗa sabon kwamandan yaƙi da ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram
Nadin Manjo Janar Ibikunle Ademola Ajose na daga cikin sauye-sauyen shugabancin soji da suka shafi wasu janar-janar 14, in ji kakakin rundunar sojin.

9 Sep, 2026
NEMA ta karɓi ’yan Nijeriya 180 da aka mayar da su gida daga Libya
Tawagar ta ƙunshi manya 169 — maza 68 da mata 101 — da kuma yara maza shida, jarirai biyar da kuma mutum ɗaya da ke fama da rashin lafiya.

9 Sep, 2026
Sojojin Nijeriya sun kama wasu da ake zargin masu kai wa ’yanta’adda kayayyaki ne a Jihar Yobe
Rundunar ta ce an gudanar da aikin ne ranar Talata, 8 ga Satumba, bayan samun bayanan sirri kan wasu kayayyakin da ake zargin za a wuce da su zuwa ga ’yanta’addan da ke aiki a yankin Yunusari-Mobbar.

8 Sep, 2026
FIFA ta tura tawaga zuwa Nijeriya don gano ko gwamnati ta tsoma baki a murabus ɗin shugabannin NFF
Wasiƙar ta nuna cewa FIFA ta zartar da wannan mataki ne a taronta na ranar 1 ga Satumba a birnin Zurich, wanda ya haɗa wakilan FIFA, CAF, da NFF, da kuma gwamnatin Nijeriya.

8 Sep, 2026
INEC za ta ƙaddamar da na’urar bibiyar shirye-shiryen zaɓe kai-tsaye
Shugaban hukumar, Farfesa Samuel Amupitan ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Legas, yayin wani taron bita na musamman da aka shirya wa Sakatarorin Gudanarwa na hukumar.

8 Sep, 2026
An kashe mutum 12, an jikkata 2 a sabon harin da aka kai wani ƙauye a Adamawa ta Nijeriya
Harin ya faru ne da safiyar ranar Litinin, kasa da makonni biyu bayan da aka kashe fiye da mutane 10 a wani harin da aka kai a ƙaramar hukumar Hong ta jihar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.


