Shugaban Sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran ya yi suka kan sabbin hare-haren Isra’ila a kan Falasdinuawa, yana mai cewa hare-haren Tel Aviv “suna zagon ƙasa da gangan” kan duk wani ƙoƙarin da ake yi na cim ma zaman lafiya a Gaza.
“A lokacin da ake da kyakkyawan fata kan yunƙurin diflomasiyya da ake yi don cim ma tsagaita wuta da ɗorewar zaman lafiya a Gaza, sabbin hare-haren Isra’ila kan fararen hula da cibiyoyin kiwon lafiya suna tarwatsa duk kokarin zuwa zaman lafiya da gangan,” in ji Duran a dandalin sada zumunta na Turkiyya NSosyal, a taranr Litinin.
Duran ya ce waɗannan hare-haren, waɗanda ba sa girmama hakkin rayuwa na mata, da yara da farar hula da ba su yi laifin komai ba, suna nunawa a fili cewa gwamnatin Benjamin Netanyahu ba ta da sha’awar kawo ƙarshen rikicin sai ƙara tsananta shi.
Ya yi kira ga al’ummar duniya da su ɗauki wani matsayi mai ƙarfi da ke kan ƙa’ida domin dakatar da waɗannan manufofin na mamaya, waɗanda ke barazana ga zaman lafiya na yankin.
“A ƙarƙashin jagorancin Shugabanmu Recep Tayyip Erdogan, Turkiyya za ta ci gaba da goyon bayan dokar ƙasa da ƙasa, da girmama ɗan’adam da halastattun haƙƙoƙin mutanen Falasdinu, tare da tallafa wa duk wani ƙoƙari da ke nufin kafa adalci da zaman lafiya mai ɗorewa,” in ji shi.
Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare ta sama duk da yarjejeniyar tsagaita wuta
Jiragen saman yaƙi na Isra’ila sun kai hari a Gaza a rana ta biyu jere a ranar Lahadi, inda suka kashe Falasdinuawa aƙalla 18, in ji ma’aikatan kiwon lafiya, duk da sanarwar Shugaban Amurka Donald Trump ta cewa an samu ci-gaba wajen aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta bara.
Tun da sanyin safiya, jiragen saman Isra’ila sun kai hari Birnin Gaza a arewa, da tsakiyar birnin Deir al-Balah da yankin kudu na Khan Younis, abin da ya jawo mafi girman adadin mutuwa a rana ɗaya cikin makonni, a cewar jami’an lafiya na Falasdinu.
Harbin Deir al-Balah ya kashe aƙalla mutane huɗu, in ji jami’an lafiya na Falasdinu, yayin da wani harin daban ya raunana mutane biyar ya kuma ƙone wasu tantuna a Mawasi, kusa da Khan Younis, a cewar hukumar bayar da agajin gaggawa ta farar hula.
An kashe wasu ma’aurata da ɗansu mai shekaru 9 a wani hari da wani gida a Mawasi, in ji jami’an Falasdinu.
An kashe wasu ma’aurata tare da ɗansu a wani harin da aka kai wani rukunin gidaje a Birnin Gaza, yayin da wasu mutane biyu suka mutu a wani harin kan wani tanti kusa da wani ofishin jakadancin Masar, in ji ma’aikatan kiwon lafiya. Daga baya a ranar Lahadi, an kashe wasu mutane biyu a gabashin unguwar Zeitoun ta birnin, kamar yadda suka bayyana.
An kashe mutum ɗaya a kusa da Jabalia a arewacin Gaza, in ji jami’an Falasdinawa.
Kwamitin Zaman Lafiya na Trump, hukumar da Amurka ke jagoranta wacce ke kula da yarjejeniyar tsagaita wuta, ta wallafa wata taswira mai sassa 15, tana mai fayyace matakan ƙarshe na aiwatar da yarjejeniyar.
Nickolay Mladenov, babban jakadan Kwamitin Zaman Lafiya na Gaza, ya ce hare-haren a fadin Gaza sun auku duk da ƙoƙarin kwamitin da masu sasanci na yunkurin samun amincewar ƙungiyoyin Falasdinu kan matakan aiwatar da shirin Trump.
Ya faɗa a wani rubutu a X cewa yana aiki tare da ɓangarori, da masu shiga tsakani da abokan hulɗa na yankin don “rage tashin hankalin da samar da yanayin aiwatar da cikakken shirin Shugaban.















