Shugaban Kamaru Paul Biya ya yi sauye-sauye a shugabancin hafsoshin sojin ƙasar, inda ya ƙara wa shugaban Dakarun Tsaron Fadar Shugaban ƙasa girma daga kanar zuwa muƙamin birgediya janar, sannan ya sauya hudu daga kwamandojin soji na haɗin gwiwa na shiyyoyi biyar na ƙasar, kamar yadda dokoki uku daban-daban na shugaban ƙasa suka nuna.
Biya, wanda shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya kwashe watanni biyu ba a gan shi ba a bainar jama’a. Ya bar Kamaru ne a ranar 7 ga watan Yuni domin abin da fadar shugaban ƙasa ta bayyana a matsayin “gajeren zama na ƙashin kai a Turai”, amma har yanzu bai koma gida ba.
Naɗe-naɗen sun haɗa da sabon kwamandan rundunar ɗaukar matakin cikin hanzari, da ƙarin girma ga Manjo Janar Ebaka Hippolyte zuwa Manjo Janar kuma Babban Hafsan Hafsoshin ƙasar, da ƙara wa kanar-kanar da dama girma zuwa matsayin birgediya janar, da kuma sauye-sauye a rundunonin sojin sama da na ƙasa bangaren motoci.
Jam’iyya mai mulki a Kamaru ta kira wani taro na musamman na manyan shugabanninta a watan da ya gabata, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba game da rashin kasancewar Biya a ƙasar.
Biya, mai shekaru 93, wanda ke mulkin ƙasar mai arzikin man fetur da koko tun shekarar 1982, yakan shafe dogon lokaci a ƙasashen waje, kodayake tsufansa ya haifar da jita-jita game da lafiyarsa, da inda yake, da kuma ikonsa na yin mulki. Tafiyar da ya yi yanzu zuwa ƙasashen waje ɗaya ce daga cikin mafi tsawo da ya taba yi.
Sai dai mai magana da yawun gwamnatin ta Kamaru, Rene Emmanuel Sadi, ya shaida wa gidan radiyon Faransa na RFI cewa “shugaban yana raye” kuma ba da daɗewa ba zai dawo gida.















