Shugaban Nijeirya, Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasar zagon ƙasa ta nemi kotu ta sake buɗe asusun gwamnatin jihar Osun tare da yin watsi ƙarar da hukuncin kotun da ya ba ta damar rufe asusun gwamantin jihar da ke kudu maso yammacin ƙasar.
Sanarwar da shugaban ya fitar ranar Alhamis wadda Mai Taimaka wa Shugaban kan Watsa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ta ce lokacin da hukumar ta ɗauki matakin kai batun kotu ya bai wa shugaban ƙasar kunya matuƙa.
“Dole na bayyana cewa na ji kunya sosai ba wai game da yadda hukumar EFCC ta yi aikinta bisa goyon bayan hukuncin kotu ba, amma sakamakon lokacin da ta ɗauki matakin,” in ji Tinubu.
Shugaban ya ce shi ya bai wa EFCC umarni ta garzaya kotu domin janye umarnin tare da janye dukkan ƙarar da ta shigar kotu kan gwamnatin jihar Osun game da batun.
“Wannan ya kasance a haka ne domin duk wani matakin da wata hukuma ta gwmanati ta ɗauka, musamman a matakin Tarayya, ana jingina shi ne gare ni, a matsayina na Shugaban Ƙasa, ko da kuwa ba ni da wata masaniya game da matakin kafin a ɗauke shi,” in ji Shugaban ƙasar.
Tinubu ya ce tun lokacin da shi ya hau ƙaragar mulki ya nanata cewa ya kamata a bar hukumomin da ke yaƙi da cin hanci da rashawa su yi ayyukansu cikin cikakken ‘yanci da ƙwarewa ba tare da tsoro ko son kai ba ko kuma katsalandan na siyasa.
“Da gan-gan na kame kaina daga ba da umarni ko kuma tsoma baki a ayyukan EFCC ko kuma ko wace hukuma ta bincike ko ta shari’a saboda na yi imani sosai cewa cibiyoyin dimokuraɗiyya da ke aiki bisa doka suna da muhimmanci ga gwamnati mai nagarta da bin doka da oda,” in ji Shugaban.
Tinubu ya ce a a matsayinsa na shugaba, ya jajirce wajen tabbatar da ganin cewa an ƙyale dukkan hukumomin gwamnati su yi aiki kamar yadda ya kamata, kuma su ɗauki duk wani mataki da ya kamata domin jagorancin da ya kamata ba tare da buƙatar sai an ba su umarni ba.
“Wannan shi ne ya sa dokoki suka samar da hukumomi tare da bayyana ikonsu,” in ji sanarwar.
Shugaban ya ce lokacin da hukumar ta kai ƙarar bai dace ba, yana mai ƙarawa da cewa jihar tana da ‘yan kawanaki ne kawai da suka rage kafin a yi zaɓen gwamnan jihar, kuma bai kamata a yi duk wani abu da zai iya sa a yi tunanin cewa ana amfani da EFCC ko wata hukuma ta gwamnati wajen katsalandan a zaɓen ba.















