Gwamnatin Jihar Kano ta musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zargin cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi watsi da Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, yayin bikin Hawan Nasarawa. Ta bayyana wannan labari a matsayin ƙarya mara tushe da aka ƙirƙira domin yaudarar jama’a da kuma haddasa rikici a tsakanin al’umma.
A cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar, an jaddada cewa babu wani raini ko wulakanci da aka yi wa sarkin. Ya bayyana cewa rashin halartar gwamnan bikin ya samo asali ne saboda wani muhimmin taron gwamnonin Nijeriya da aka gudanar a Legas wanda ya wajaba ya halarta.
Duk da hakan, gwamnan ya sanar da sarkin tun da wuri kuma ya tura manyan jami’an gwamnati su wakilce shi, ciki har da Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano. Haka kuma ya halarci wasu muhimman bukukuwan Sallah, ciki har da sallar Idi da Hawan Daushe, tare da karɓar wasu sarakunan gargajiya a jihar.
Gwamnatin ta jaddada cewa dangantaka tsakanin gwamnatin Kano da Masarautar Kano na nan daram, tana gudana cikin mutunta juna da haɗin kai, ba tare da wata matsala ko rashin fahimta ba.














