Nijar ta gindaya sharruɗa biyu da ba za ta yarda a tattauna su ba ga Benin a matsayin abin da ake buƙata domin sake buɗe kan iyakar ƙasar da Benin.
Rahotanni sun ce a ranar Lahadi ce wata babbar tawaga ta gabatar da waɗannan buƙatun yayin tattaunawar diflomasiyya ranar Lahadi.
Manjo Janar Mohamed Toumba, wani babban mamba a majalisar ceton ƙasa ta mulkin sojin ƙasar Nijar (CNSP) kuma minista tsaron cikin gida ya bayyana cewa sake buɗe kan iyakar ƙasar ya dogara ga amincewar Benin da waɗannan ƙa’idoji waɗanda Yamai ta bayyana cewa suna da muhimmanci ga tsirar ƙasar.
Sharruɗa biyun masu tsauri su ne:
Yarjejeniyar tsaro a hukumance: Wata yarjejeniyar da ta zama wajibi a mutunta ta wadda za ta samar da yarjejeniyar bisa ƙa’idar rashin fara kai hari, tabbatar da cewa ba a yi amfani da ƙasar ɗaya daga cikinsu ba wajen kai hari ga ɗaya ko yi wa ɗaya ƙasar zagon ƙasa ko kuma aikata wani aiki na tayar da hankali a ɗaya ƙasar.
Tsantsar tabbatar da fayyace gaskiya game da kafa kayayyakin sojin ƙetare: Cikakken bayani game da dakarun sojin ƙetare da aka tura kusa da kan iyakokin ƙasashen biyu, tare da kafa wata runduna ta haɗaka ta tattara bayanan sirri nan take domin haɗa bayanai da kuma yaƙar ta’addancin kan iyaka tare.
Waɗanan buƙatun masu tsauri sun samo asali ne daga rabbarbuwar kai mai muni da aka samu bayan juyin mulkin Nijar na ranar 26 ga watan Yuli na shekarar 2023.
Kafin juyin mulkin, maƙwabtan suna da yarjejeniyar yaƙi da ta’addanci tare. Sai dai kuma, daga baya CNSP ta warware yarjejeniyar kuma ta nanata zargin Benin da karɓar baƙuncin sansanonin sojin Faransa domin tayar da hankali a Nijar — wani zargin da gwamnatin shugaban Benin Patrice Talon ta musanta.
Zama mai muhimmanci na wannan ƙarshen makon a Cotonou ya samu jagoranci na mai magana da yawun gwamnatin Benin Olushegun Adjadi Bakari.
Ƙwararrun masana daga fannin diflomasiyya da makamashi da tsaro da kwastom sun yi aiki a ɓoye wajen sauya wata ɗaya na tattaunawar farko-farko zuwa wani tsari na cim ma dawowa da alaƙa.
An kafa tattaunawar ne bisa tsarin da aka samar da farkon wannan watan yayin ziyarar Shugaban Benin zuwa ga shugaban Nijar Abdourahamane Tiani.
Duk da tsaurin wa’adin, an ƙarƙare ƙarshen makon da kyakkyawan fata. Ɓangarorin biyu sun bayyana buri mai ƙarfi na rage matsin tattalin arziki mai yawa da rufe kan iyakar ƙasashen ya janyo wa mutanensu.
A halin yanzu tattaunawar ta tsaya domin bai wa hukumomin Benin lokaci na yin cikakken nazari kan sharruɗan tsaro na Yamai kafin shirya wata ganawa domin ƙarasa tabbatar da yarjejeniyar.















