Jami’an tsaron Nijeriya sun ceto daliban da aka yi garkuwa da su a Jihar Oyo

Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Kafafen Sada Zumunta, Dada Olusegun ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a yammacin ranar Jumma’a.

Newstimehub

Newstimehub

10 Jul, 2026

8ed760a5 cf67 4c16 a73a 0a8d1d0f4eb8 1783705159997

An ceto tare da kuɓutar da dukan ɗalibai da malamai da aka sace yayin harin da aka kai wa al’ummar Ahoro-Esiele da ke Ƙaramar Hukumar Oriire a Jihar Oyo ranar 15 ga Mayu.

Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Kafafen Sada Zumunta, Dada Olusegun ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a yammacin ranar Jumma’a.

An sace mutanen ne bayan wasu ‘yanbindiga ɗauke da muggan makamai sun mamaye al’ummar, inda suka yi garkuwa da ɗalibai 46, malamai da kuma shugaban wata makarantar sakandare, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma a faɗin ƙasar.

Lamarin ya ƙara muni kwanaki bayan sace mutanen, lokacin da masu garkuwar suka fille kan ɗaya daga cikin malaman da aka sace, Michael Oyedokun.