Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa an yi motsin ƙasa a wasu sassan Abuja, babban birnin tarayyar ƙasar a ranar Talata.
Ministan Ma’adinai na ƙasar Dele Alake ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da mai magana da yawunsa Lara Owoeye-Wise ta fitar ranar Laraba.
Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Nijeriya (NGSA) ta ce ofishinta da ke yankin Utako ya ba da rahoton jin motsin ƙasa da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata.
Hukumar ta ce lamarin ya auku ne a yanki mai nisan kilomita ɗaya ta ƙasa kuma ya yi tafiyar kilomita huɗu cikin daƙiƙa biyar.
A cewar NGSA, motsin ƙasar ya kai ƙarfin maki 1 zuwa 2 a ma’aunin Mercalli, inda ta bayyana yanayin da mai sauƙi da ba zai iya haifar da lalacewar gine-gine ko barazana ga rayuka da dukiyoyi ba.
Sanarwar ministan ta ce tuni aka ɗauki matakan gaggawa na gudanar da bincike domin tabbatar da tsaron lafiya da kadarorin mazauna birnin.
Kazalika Dele Alake ya umarci hukumar NGSA da ta samar da sabbin bayanai a-kai-a-kai game da yanayin domin ci gaba da tantance ainihin abi da ya faru da kuma yiwuwar yin aiki tare da sauran hukumomin gwamnati.
Ministan ya yi kira ga mazauna birnin da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullun ba tare da wata damuwa ba
Duk da cewa Nijeriya ba ta cikin manyan yankunan da ake samun iftila’in girgizar ƙasa a duniya, amma ana samun motsin ƙasa mara ƙarfi a wasu lokutan a Abuja da wasu jihohi, wanda hakan ke nuna buƙatar ci gaba da sa ido kan yiwuwar aukuwar girgizar ƙasa da kuma shirye-shiryen gaggawa.















