Fafaroma Leo XIV ya nemi afuwa kan rawar da Cocin Katolika ya taka a cinikin bayi tsakanin nahiyoyi

Babu wani shugaban cocin Katolika da ya taɓa neman afuwa a bainar jama’a kan rawar da tsofaffin fafaromomi suka taka wajen bai wa sarakunan Turai cikakken iko na bautar da miliyoyin mutane, musamman ‘yan Afirka.

Newstimehub

Newstimehub

25 May, 2026

2026 05 25t110806z 1577482378 rc2bglamet21 rtrmadp 3 pope encyclical presentation

Fafaroma Leo XIV ya gabatar da wata muhimmiyar neman afuwa ta tarihi kan rawar da Holy See ta taka wajen halasta bautar da mutane, da kuma gazawar da ta yi na yin Allah wadai da hakan tsawon ƙarnuka, yana mai kiran tarihin Vatican ɗin da “wani rauni a ƙwaƙwalwar Kiristanci.”

Fafaromomi na baya sun taɓa neman afuwa kan rawar da Kiristoci suka taka a cinikin bayi tsakanin nahiyoyin Tekun Atlantika. Amma babu wani Fafaroma da ya taɓa amincewa a bainar jama’a — balle ya nemi afuwa — kan rawar da tsofaffin Fafaromomi da kansu suka taka wajen bai wa sarakunan Turai cikakken iko na murƙushewa da bautar da waɗanda suka kira “kafirai.”

Fafaroman wanda shi ne Ba’amurke na farko a tarihi da ya taba zama fafroma, wanda tarihin iyalinsa ya haɗa da bayi da masu mallakar bayi, ya gabatar da wannan neman afuwar ne ranar Litinin a cikin wasiƙarsa ta farko ga duniya baki ɗaya mai suna Magnifica Humanitas (Babban Darajar Ɗan’Adam), wadda aka fitar a wannan rana.

Wannan doguwar sanarwa tana magana ne kan kare bil’adama a wannan zamani da ake ƙara dogaro da Ƙirƙirarriyar Basira. Fafaroma Leo ya ambaci cinikin bayi tsakanin nahiyoyin Atlantika ne dangane da abin da ya kira sabbin nau’o’in bautar da mulkin mallaka da juyin juya halin da fasahar zamani ke haifarwa, kamar aikin wahala mara tsari da ake buƙata wajen haƙo ma’adanai masu wuya da ake amfani da su wajen ƙera na’urorin AI.

Ina neman afuwa”

Ta haka ne Fafaroma Leo XIV ya mayar da martani ga shekaru da dama na kiraye-kirayen da bakaken Katolika na Amurka, masu fafutuka da masana suka yi wa Holy See domin ta nemi gafara kan rawar da ta taka a cinikin bayi a lokacin mulkin mallaka.

“Ba zai yiwu mutum ya yi tunani kan irin wahala da wulaƙancin da mutane da yawa suka sha ba tare da jin baƙin ciki mai zurfi ba, alhali kuwa suna da daraja mara misaltuwa a matsayin halittun da Ubangiji ke ƙauna ba tare da iyaka ba,” in ji Leo. “Saboda haka, a madadin Cocin, ina neman gafara da gaske.”

Vatican ta dage cewa koyaushe tana kare mutuncin dukkan bil’adama a matsayin bayin Allah. Sai dai wasu umarnin Vatican da aka bayar a ƙarni na 15 sun bai wa sarakunan Portugal izinin mamaye Afirka da nahiyoyin Amurka tare da bautar da waɗanda ba Kiristoci ba.