Amurka ta sa takunkumi kan wani ɗan canji dan Nijeriya da wasu kamfanoni kan zargin tallafa wa Daesh

Amurka ta bayyana cewa babban wanda ake zargi da tallafa wa Daesh ɗin ta hanyar canjin kuɗi ɗan Nijeriya ne, yayin da uku daga cikin kamfanoni shida da aka sanyawa takunkumin suke da rassa a Nijeriya, biyu a Jihar Lagos, guda ɗaya kuma a Jihar Kano.

Newstimehub

Newstimehub

24 Jun, 2026

trump 31 74

Ƙasar Amurka ta ƙaƙaba wa wani mutum mazaunin Nijeriya takunkumi, inda ake zarginsa da taimaka wa ƙungiyar Daesh wajen tura kuɗaɗe ta iyakokin ƙasashe daban-daban ta hanyar sana’ar canjin kuɗi.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, Tommy Pigott, ya bayyana cewa ɗan Nijeriyar yana ɗaya daga cikin mutane uku da kuma kamfanoni guda shida da aka sanya wa takunkumin saboda zargin sauƙaƙa hanyoyin samar da kuɗaɗe ga ƙungiyar Daesh a faɗin yankunan Turai, Gabas Ta Tsakiya, da kuma Yammacin Afirka.

Pigott ya bayyana cewa mutanen da takunkumin ya shafa sun haɗa da wani mai taimaka wa ƙungiyar, mazaunin ƙasar Faransa wanda ake zargi da samar da bayanan abubuwan fashewa ga magoya bayan Daesh, da wani mai gudanar da harkoki mazaunin ƙasar Siriya wanda ake zargi da yin amfani da kuɗaɗen intanet na ‘cryptocurrency’ wajen tura kuɗaɗe ga abokan hulɗar Daesh a ƙasashe da dama, haɗi da Amurka, da kuma wani mai taimaka wa ƙungiyar mazaunin Nijeriya wanda aka yi amfani da sana’arsa ta canjin kuɗi wajen tura kuɗaɗe ga ƙungiyar.

Amurka ta bayyana cewa babban wanda ake zargi da tallafa wa Daesh ɗin ta hanyar canjin kuɗi ɗan Nijeriya ne, yayin da uku daga cikin kamfanoni shida da aka sanyawa takunkumin suke da rassa a Nijeriya, biyu a Jihar Lagos, guda ɗaya kuma a Jihar Kano.