Hukumar yaki da cin hanci ta Najeriya (EFCC) ta fitar da gargadi ga masu kirkirar bidiyo da sauran masu amfani da kafafen sada zumunta kan amfani da sunanta da alamominta ba tare da izini ba. Hukumar ta ce ta lura da karuwar bidiyoyi da ke amfani da sunanta, tambari da kayan aikinta, abin da ta bayyana a matsayin abin da ke bata mata suna da kuma karkatar da yadda take aiki.
EFCC ta jaddada cewa ba ta ba da izini ga irin wadannan bidiyoyi ba, kuma ba ta dauki nauyin ko amincewa da kowanne irin wasan barkwanci, drama ko wani abun ciki da ke amfani da sunanta ba tare da rubutaccen izini ba. Ta bukaci duk wanda ke yin hakan da ya dakatar nan take, tana mai gargadin cewa duk wanda ya karya wannan umarni zai fuskanci hukunci a gaban kotu.
Hukumar ta kara da cewa dole ne a nemi izini a rubuce kafin amfani da sunanta, tambarinta, ko kayan aikinta a kowanne irin shiri, domin kare martabarta da kuma hana rudani a tsakanin jama’a.
MAJIYAR LABARI: NEWSTIMEHUB














