Shugaban Dangote Group, Aliko Dangote, ya jaddada bukatar gaggauta saka jari a masana’antu da kuma samar da ingantaccen wutar lantarki, yana mai cewa Najeriya dole ta fara ƙera, tsara da gina abin da take amfani da shi domin samun cikakkiyar ‘yancin tattalin arziki. Ya bayyana haka ne a wajen taron Nigerian Academy of Engineering a Lagos, inda aka karrama shi a matsayin Distinguished Honorary Fellow.
Dangote ya ce babu yiwuwar cimma ‘yancin tattalin arziki ba tare da ikon fasaha ba, yana mai kira ga injiniyoyi da su taka rawar gani wajen gina hanyoyin wutar lantarki da ƙarfafa masana’antu. Ya bayyana cewa wutar lantarki na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban masana’antu, yana mai ƙarfafa haɗin kai domin gina Najeriya da za ta amfani kowa, ba wasu kaɗan ba.
Ya kuma nuna cewa sabbin kirkire-kirkire na injiniya sun taka muhimmiyar rawa wajen gina matatar mai ta Dangote, wadda ke da ƙarfin aiki fiye da yawancin makamantansu a duniya. A cewarsa, burinsu shi ne su sa Najeriya da Afirka gaba ɗaya su daina dogaro da kayayyakin da ake shigo da su daga waje, tare da tabbatar da cewa hakan zai yiwu a aikace.
Sai dai ya yi gargadi kan tasirin fasahar basirar wucin gadi (AI), yana cewa na iya sauya wasu fannoni na aikin injiniya, don haka ya bukaci ƙwararru su shiga gaba wajen tsara yadda za a yi amfani da ita. A wani bangare kuma, ya bayyana shirin gina sabuwar matatar mai a Gabashin Afirka mai ƙarfin sarrafa ganga 650,000 a rana, a cikin wani shirin zuba jari na dala biliyan 40, wanda zai dogara da goyon bayan gwamnati.
MAJIYAR LABARI: NEWSTIMEHUB













