Wasu masana kimiyya a ƙasar China na aiki kan wata sabuwar hanya da za ta iya sauya yadda ake samar da man jirgin sama, inda suke ƙoƙarin maida iskar carbon dioxide (CO₂) zuwa man fetur. Wannan ci gaba na iya taimakawa rage tsadar mai da kuma gurbatar muhalli da ke damun masana’antar jiragen sama a duniya.
Binciken, wanda Shanghai Advanced Research Institute karkashin Chinese Academy of Sciences ke jagoranta, ya mayar da hankali ne kan sauya iskar da ke gurbata muhalli zuwa man da za a iya amfani da shi. A takaice, ana daukar CO₂ da ruwa a maida su man mai kama da wanda jirage ke amfani da shi, kamar dai an juya tsarin konewar mai baya.
Wannan bincike ya zo ne a daidai lokacin da farashin mai ke ƙaruwa a duniya sakamakon rikice-rikicen siyasa, musamman wadanda suka shafi Amurka, Isra’ila da Iran, wanda ya kawo tangarda ga samar da makamashi. Sakamakon binciken da aka wallafa a mujallar American Chemical Society ACS Catalysis ya nuna ci gaba wajen samar da sinadaran carbon masu tsawo da ake bukata domin man jirgin sama cikin inganci.
Idan wannan fasaha ta yi nasara a kasuwa, za ta iya rage dogaro da man fetur na gargajiya, rage hayakin carbon ta hanyar sake amfani da CO₂, da kuma taimakawa wajen daidaita farashin mai. Gabaɗaya, wannan kirkira na iya zama babbar nasara, inda za a samu makamashi mai tsafta tare da rage tsadar mai a daya daga cikin manyan masana’antun da ke amfani da makamashi sosai.
MAJIYAR LABARI: NEWSTIMEHUB












