Asusun Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) a ranar ya ce ce sauye-sauyen da gwamnatin Nijeriya ta aiwatar sun ƙarfafa tattalin arzikin ƙasar, amma ya yi gargaɗin cewa fiye da kashi 60 cikin 100 na ’yan Nijeriya yanzu suna rayuwa cikin talauci.
Tun bayan hawansa mulki fiye da shekaru uku da suka gabata, Shugaba Bola Tinubu ya cire tallafin man fetur mai tsada wanda ya daɗe yana sa farashin fetur ya yi sauƙi a ƙasar, sannan ya sassauta tsarin canjin kuɗin ƙasar da kuma sake fasalin tsarin haraji.
Ko da yake masana tattalin arziki sun ce waɗannan sauye-sauyen sun daɗe suna buƙatar a aiwatar da su, talauci ya ci gaba da ƙaruwa, inda ya shafi kashi 63 cikin 100 na al’ummar ƙasar zuwa ƙarshen shekarar 2025.
IMF ya ƙara da cewa fiye da mutane miliyan 27 sun fuskanci matsalar rashin wadataccen abinci a shekarar.
“A cikin shekaru uku da suka gabata, manyan sauye-sauyen da aka aiwatar sun haifar da ingantattun sakamakon tattalin arziki tare da ƙarfafa juriyar tattalin arzikin ƙasar,” in ji IMF a cikin wata sanarwa bayan nazarinsa na shekara-shekara kan tattalin arzikin Nijeriya.
Sai dai ya ƙara da cewa, “duk da haka, rayuwa tana ci gaba da kasancewa mai wahala ga ’yan Nijeriya da dama.”
Talauci ya shafe shekaru yana ƙaruwa a Nijeriya, ƙasa mafi yawan jama’a a Afirka. A rahotonsa na baya-bayan nan, Bankin Duniya ya bayyana cewa kusan kashi 61 cikin 100 na al’ummar ƙasar suna rayuwa cikin talauci, idan aka kwatanta da kashi 40 cikin 100 a shekarar 2019.
Bankin Duniya ya kuma lura cewa kusan kashi uku cikin huɗu na wannan ƙarin talauci ya faru ne kafin shekarar 2023, lokacin da aka rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.















