Wata kotun daukaka kara ta Amurka ta ba da damar ci gaba da sauraran dubban kararraki kan kamfanonin fasaha na Meta da Alphabet’s Google da ByteDance’s TikTok da sauran wasu kamfanonin sada zumunta kan ikirarin cewa sun tsara shafukansu ta yadda matasa za su jarabtu da su a yayin amfani.
Kotun ta 9 da ke San Francisco a ranar Litinin ta yi watsi da yunkurin kamfanonin na soke hukuncin wata karamar kotu da ya tilasta musu fuskantar shari’o’i fiye da 3,000 kan ikirarin da aka shigar a kotun tarayya, inda ta kammala da cewa daukaka karar ta zo da wuri a shari’ar.
Wadanda ake karar, ciki har kafar Snapchat na Snap Inc, sun ƙalubalanci Sashe na 230 na Dokar Sadarwa ta 1996 – wanda galibi ke kare kamfanonin sada zumunta daga ikirari kan abubuwan da masu amfani da shufukansu suke wallafawa – haka kuma ta hana kararrakin da ke ikirarin cewa sun gaza gargadin jama’a game da yanayin jarabar shafukan nasu.
Yawancin kararrakin suna zuwa ne bayan an kammala shari’a ko kuma yanke hukunci. Meta ta ƙalubance Sashe na 230 da ya ba ta kariya mai yawa kuma ya kamata ta iya ɗaukaka ƙara nan take ga hukuncin kotun, sai dai ɓangaren Kotun 9 ya ce Sashe na 230 ya ba da kariya ga wanda ya dauki alhaki, ba wai kariya daga ƙararraki ba, don haka ƙarar da aka ɗaukaka ta yi wuri.
Kotun ta kuma yi watsi da buƙatar Meta na ɗage shari’ar da za a fara a ranar Laraba kan ƙarar da manyan lauyoyin jihohi 29 suka shigar, inda suka zargi kamfanin da tattara da kuma amfani da bayanan yara ba bisa ƙa’ida ba, sannan ya tsara shafukansa ta yadda za su zama jaraba ga matasa da kuma ɓatar da masu amfani game da amincinsu.
Kamfanin ya bayyana cewa bai kamata a ci gaba da shari’ar ba yayin da ake ci gaba da daukaka kara.
Wakilin Meta kuma mai magana da yawun manyan lauyoyin da ke ɗaukaka ƙarar ba su amsa buƙatun yin tsokaci nan take ba.
Da gangan shafukan sada zumunta suke mayar da hankali kan matasa
Gwamnatocin jihohi da na ƙananan hukumomi da makarantun gundumomi da kuma daidaikun mutane ne suka shigar da ƙarar, inda suke zargin cewa da gangan kamfanonin kafofin sada zumunta suke sanya shafukansu su zama jaraba ga matasa, wanda hakan ke ba da gudummawa ga ƙaruwar yanayin baƙin ciki da damuwa da kuma faɗaɗa matsalar lafiyar kwakwalwa tsakanin matasan Amurka a cikin ‘yan shekarun nan.
Iyaye da makarantun gundumomi da gwamnatocin jihohi da sauran waɗanda suka shigar da ƙara sun bayyana cewa hukuncin kotun shari’a ba shi ne na ƙarshe ba, don haka ba za a iya ɗaukaka ƙara ba a yanzu.
Sun kuma yi watsi da hujjojin kamfanonin game da Sashe na 230, inda suka ce ba ya cikin ikirarin da ya shafi yadda suke aiki da kuma tsara manhajojinsu.
Ƙararrakin waɗanda aka mayar gaban Alkalin Gundumar Amurka Yvonne Gonzalez Rogers a Oakland da ke California, sun nemi diyya da hukunci daga kamfanonin.
Kamfanonin sun ɗaukaka ƙarar umarnin Rogers a shekarar 2023 da 2024 wanda ya ba da damar a ci gaba da sauraran ƙarar.
Kamfanonin suna fuskantar ɗaruruwan irin waɗannan ƙararraki a kotunan jihar, ciki har da kimanin ƙararraki 3,300 da ake saurara a kotun jihar California.
Wani alkalin Los Angeles a watan Maris ya gano cewa Meta da Google ba sa sa ido kan tsare-tsaren kafofinsu da ke cutar da matasa, a ƙarar farko da aka saurara a California da kuma hukuncin da masu saurarar ƙarar suka dauka.
Alkalin ya yanke hukuncin baiwa wata matashiya mai shekaru 20 diyyar dala miliyan 6 saboda ta ce tana fama da jarrabar Instagram da YouTube tun tana ƙarama.
Meta ta kuma yi rashin nasara a dukkan matakai biyu na wata muhimmiyar shari’a da New Mexico ta shigar a kotun jihar.
A watan Maris, wani alkali ya umarci kamfanin da ya biya diyyar dala miliyan 375 bayan ya gano cewa ya yaudari masu amfani game da amincin shafukansa.
A ranar Alhamis, wani alkali ya gano cewa Meta ta haifar da matsala ga jama’a kuma ya umarce ta da ta biya ƙarin diyyar dala miliyan 567 tare da aiwatar da matakan tsaro ga matasa.
Sai dai Meta da Google, waɗanda suka musanta ikirarin waɗannan shari’o’in, sun ce za su ɗaukaka ƙara.













