Ministocin makamashi na ƙasashe mambobin ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) na ganawa a Accra babban birnin ƙasar Ghana domin nazari kan dokoki na ajiyar makamashi cikin batura da na tafiyar da kasuwannin lantarki.
Dokokin da ministocin ke nazari a kai na son daidaita fannonin makamashi a ƙasashen ƙungiyar da tallafa wa ci-gaban makamashi da ake iya sabutawa da kuma ƙarfafa kasuwar makamashi ta yankin.
Na farko daga ciki shi ne umarni na tsarin adana makamashi na batura (BESS) da fasahohi masu kama da shi da wanda ake sa ran za su taimaka wajen haɗa hasken rana da sauran hanyoyin samun makamashi na sabuntawa da tsarin layin lantarki.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar Ghana ya ce ta biyun ita ce gyara dokar harajin lantarki na yanki domin ba da isasshen kuɗi ga hukumomin kula da makamashi na yanki domin aiwatar da ayyukansu na sa ido yadda ya kamata.
Kwamishinan ababen more rayuwa makamashi da dijital na ECOWAS Amin Amidu Sulemani ya ce dokokin za su samar da hanya ta haɗin gwiwa wajen inganta makamashi a faɗin yankin.
“Idan muka yi aiki daban daban za a sha wahala a fannin makamashi, dole mu yi aiki a matsayinmu na yanki da kuma haɗaɗɗiyar ƙungiya,” kamar yadda ya bayyana wa manema labarai a taron ranar Alhamis.
Ya ce adana makamashi a batura na da muhimmanci wajen taimaka wa samar da lantarki da hasken rana, musamman a lokutan da aka fi buƙatar lantarki, kuma zai iya rage tsadar samar da makamashi.
Dr John Abdulai Jinapor, ministan makamashi da koma amfani da makamashin da ake iya sabuntawa na Ghana ya ce haɗin kan yanki na da muhimmanci wajen magance matsalolin da ke tattare da samun lantarki da girki mai tsafta da makamashi mai ɗorewa.
Ya ce Ghana na amfani da mafita na adana makamashi a batura domin iya magance matsalar lokacin da aka fi buƙatar lantarki da kuma inganta amfani da ikon samar da lantarki da ƙasar ke da shi yadda ya dace.
Ya ce giɓin da ake samu tsakanin lokacin da aka fi buƙatar lantarki da lokacin da aka fi rashin buƙatarsa ya kan iya kai megawatt 800 a wasu lokuta.
Ya ce ƙasar ta kammala tayin farashin kwangila na samar da megawatt 200 na makamashin hasken rana kuma tana shirin sake samar da wani hasken rana mai ƙarfin megawatt 200 domin iya biyan buƙatar lokutan da aka fi ɓuƙatar wuta.
“Makomar tsaron makamshi ba kawai iya makamashin da muka iya samarwa ba ne, sai dai yadda muka yi amfani da basira wajen sarrafa makamashin da muke da shi,” in ji ministan.















