Kenya ta tabbatar da mutuwar mutum na biyu daga cutar Ebola

Matar ta fara nuna alamun cutar ne kwanaki 10 da suka wuce, inda aka fara ba ta kulawa a sashen kula da cututtuka masu yaɗuwa da ke Nairobi, babban birnin ƙasar.

Newstimehub

Newstimehub

24 Oct, 2026

7ec6c872 e570 442e b6d5 b5c000543dab 1792311613822

Ma’aikatar Lafiya ta Kenya ta sanar da mutuwar mutum na biyu sakamakon cutar Ebola a ƙasar, inda ta ce wata mata mai shekara 65, wadda take da kusanci da mutum na farko da ya kamu da cutar, ta rasu bayan ta fara nuna alamun cutar tana tsare a keɓe.

Matar ta fara nuna alamun cutar ne kwanaki 10 da suka wuce, inda aka fara ba ta kulawa a sashen kula da cututtuka masu yaɗuwa da ke Nairobi, babban birnin ƙasar.

Ma’aikatar ta ce ma’aikatan lafiya “sun yi duk abin da za su iya domin ceton rayuwarta”, amma ta rasu a yammacin ranar Jumma’a.

An sanar da iyalanta game da mutuwar, kuma ma’aikatar ta ce za ta shirya jana’iza cikin aminci da mutuntata, tare da tuntuɓar ’yan uwanta.

Sauran mutane bakwai da suka kamu da Ebola suna yi jinya a cibiyoyin keɓe marasa lafiya guda biyu. Ba a samu sabon rahoton wani da ya kamu da cutar ba.

Za a sallami waɗanda ke keɓe ba tare da alamun cutar ba

Kenya ta sanar da samun mutum na farko da ya kamu da Ebola a tarihinta a ranar 6 ga Oktoba, bayan wani ɗan ƙasar mai shekara 40, wanda ke zaune a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, ya yi tafiya zuwa Kenya ta Uganda, inda ya isa ranar 3 ga Oktoba.

Wani ɗan uwansa ne ya kai shi Asibitin Nairobi, inda aka tabbatar da cewa ya kamu da Ebola a ranar 5 ga Oktoba, kuma ya rasu a wannan rana.

Hukumomi sun gano kusan mutane 135 da suka yi hulɗa da mara lafiyar na farko, inda aka killace mutum 118. An tabbatar da cewa mutane takwas sun kamu da cutar yayin da suke keɓe, ciki har da ma’aikatan lafiya huɗu da ’yan uwa huɗu na kusa da marigayin.

Ma’aikatar Lafiya ta ce za a fara sallamar wasu daga cikin waɗanda aka killace daga ranar Asabar, bayan sun kammala kwanaki 21 na keɓewa ba tare da nuna alamun cutar ba.

Cutar Ebola tana da saurin yaɗuwa sosai, kuma tana yaɗuwa ta hanyar taɓa ruwan jikin mutumin da ya kamu da cutar kai tsaye, ciki har da jini da amai, ko kuma ta hanyar taɓa kayayyaki da wuraren da suka gurɓace, kamar shimfiɗar gado da tufafi.

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo na fama da ɓarkewar Ebola mafi muni ta fuskar yawan mace-mace, inda aƙalla mutane 4,000 suka mutu tun daga watan Mayu.