Kasar Togo ta samu umarni daga African Union domin gabatar da bukata a United Nations kan a gyara yadda ake nuna nahiyar Afrika a taswirar duniya. Wannan mataki na nufin gyara tsofaffin kuskure da suka dade suna rage girman Afrika a idon duniya.
A cewar Robert Dussey, wannan yunƙuri ya samo asali ne daga fahimtar cewa taswirorin da aka fi amfani da su ba sa nuna girman Afrika daidai. Duk da cewa ita ce nahiyar ta biyu mafi girma da fiye da kilomita miliyan 30, sau da yawa ana nuna ta karama saboda irin tsarin zane na taswira da ake amfani da shi.
Togo na shirin gabatar da kuduri a Majalisar Dinkin Duniya domin tabbatar da cewa ana wakiltar Afrika bisa gaskiyar kimiyya. Ba wai gyaran fasaha kawai ba ne, har ma yana da alaka da yadda ake kallon muhimmancin Afrika a duniya, musamman a fannin siyasa da tattalin arziki.
Jami’ai sun ce irin wannan kuskuren na taswira na iya rage darajar nahiyar a idon duniya, yana shafar yadda ake fahimtar ta a fannoni daban-daban. Saboda haka, wannan yunkuri na nufin inganta sahihin hoto na Afrika da kuma tabbatar da cewa an ba ta matsayi daidai a duniya.
Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB














