Rundunar sojin Nijar ta ce ta yi nasarar kashe wani ƙasurgumin ɗan Boko Haram Ibrahim Bakura, wanda ake kira Abu Umaima.
Wata sanarwar da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Alhamis ta ce dakarunta sun yi nasarar kashe ɗan Boko Haram ɗin ne a wani hari na musamman da ta kai tsibirin Shilawa a yankin Tafkin Chadi da safiyar ranar 15 ga watan Agusta.
Taƙaitacciyar sanarwar da rundunar sojin ta Jamhuriyar Nijar ta fitar ta bayyana harin sama na sojin a matsayin wanda ba a saba kai irinsa ba.
Rahotanni sun nuna cewa Ibrahim Bakura ya jagoranci wani ɓangare na Boko Haram bayan mutuwar Abubakar Shekau, kuma ya tafi yankin tafkin Chadi da ke cikin jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar da mayaƙansa.
Kazalika Bakura, wanda asalin sunansa Ibrahim Mahamadu, mai shekara 40 ɗan asalin Nijeriya ne, kamar yadda wasu rahotanni suka ambato sojin Nijar na cewa.