Za a fara taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi, COP31, a ranar Litinin a birnin Antalya da ke gabar Tekun Bahar Rum na Turkiyya, yayin da ake ƙara matsa wa gwamnatoci lamba su sauya alƙawuran da suka ɗauka kan sauyin yanayi zuwa matakan aiki, tare da ƙara tallafin kuɗi ga ƙasashen da suka fi fuskantar illolinsa.
Taron, wanda zai gudana daga ranar 9 zuwa 20 ga watan Nuwamba, zai haɗa shugabannin ƙasashe, ministoci, masu tsara manufofi, masana kimiyya da wakilan ƙungiyoyin farar hula daga sassan duniya domin tattauna hanyoyin rage fitar da hayaki mai gurɓata muhalli, daidaita al’umma da illolin sauyin yanayi da kuma samar da jarin da ake buƙata domin yaƙi da matsalar.
Turkiyya ce ke riƙe da shugabancin taron, yayin da Ministan Sauyin Yanayi da Makamashi na Australia, Chris Bowen, zai jagoranci tattaunawar. Haka kuma, an tsara gudanar da taron shugabannin ƙasashe daga ranar 11 zuwa 12 ga watan Nuwamba.
Ƙarƙashin taken “COP na Gaba – COP na Aiwatarwa”, taron na da burin sauya alƙawuran da aka ɗauka kan sauyin yanayi zuwa sakamako na zahiri da za a iya aunawa.
Abubuwan da za su kasance kan gaba a ajandar shugabancin taron sun haɗa da samar da makamashi mai tsafta da faɗaɗa samar da wutar lantarki, kawar da shara, rage fitar da iskar methane, gina birane masu jure wa illolin sauyin yanayi, bunƙasa masana’antun da ba sa gurɓata muhalli, tabbatar da wadatar abinci da kuma kare tekuna.
Sauran batutuwan da za a mayar da hankali a kai sun haɗa da ilimantar da matasa, inganta tsarin kiwon lafiya domin ya jure wa illolin sauyin yanayi, ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashe kan sauyin yanayi da bambancin halittu, da kuma yaƙi da lalacewar ƙasa.
Daga cikin muradun da ake son cimmawa nan da shekarar 2035 akwai ƙara kaso na wutar lantarki a jimillar makamashin da duniya ke amfani da shi zuwa kashi 35 cikin 100, rage yawan makamashin da gine-gine ke amfani da shi da aƙalla kashi 25 cikin 100, da kuma ƙara kaso na ma’adinan da ake sake amfani da su bayan an sarrafa su a baya zuwa kashi 15 cikin 100 na jimillar ma’adinan duniya.
Samar da kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi da rage dogaro da makamashin burbushin ƙasa na daga cikin manyan ƙalubale
Masu tattaunawa kan yarjejeniyoyin sauyin yanayi na ci gaba da samun saɓani kan yadda za a samar da kuɗaɗen tallafa wa ƙasashe masu tasowa, da kuma matakan gaggauta sauya sheƙa daga amfani da makamashin burbushin ƙasa, musamman mai da iskar gas. Wannan na zuwa ne bayan COP30 ta gaza cimma matsaya kan wasu muhimman batutuwan.
Rahoton Shirin Muhalli na Majalisar Ɗinkin Duniya na shekarar 2026 kan gibin rage hayaƙi ya yi hasashen cewa zafin duniya na iya ƙaruwa da kimanin digiri 2.6 a ma’aunin Celsius nan da ƙarshen wannan ƙarni, ko da ƙasashe sun aiwatar da alƙawuran da suka ɗauka na rage hayaƙi. Wannan zai haura iyakar da yarjejeniyar Paris ta tanada.
Rahoton ya kuma yi kiyasin cewa ƙasashe masu tasowa za su buƙaci kimanin dala biliyan 305 a kowace shekara nan da shekarar 2035 domin daidaita kansu da illolin sauyin yanayi. Sai dai kuɗaɗen da aka samar ta hanyar tsarin tallafin daidaita yanayi na ƙasashen duniya sun tsaya tsakanin dala biliyan 28.2 da dala biliyan 31.7 a shekarar 2024.
Taron na zuwa ne bayan shekara guda da aka fuskanci munanan ambaliyar ruwa, matsanancin zafi da fari a sassan duniya, lamarin da ya ƙara ƙarfafa kiraye-kirayen gaggauta rage hayaƙin da ke gurɓata muhalli da kuma ƙara tallafin kuɗi ga ƙasashen da suka fi fuskantar illolin sauyin yanayi.














