Turkiyya na shirin karbar bakuncin babban taron COP31 kan sauyin yanayi a Antalya

Taron da za a gudanar daga ranar 9 zuwa 20 ga Nuwamba, na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwar ƙasashen duniya da inganta ɗaukar nauyin yaƙi da sauyin yanayi tare, da mayar da alkawuran da aka ɗauka zuwa matakai na zahiri da za a iya aunawa.

Newstimehub

Newstimehub

9 Nov, 2026

bd22c38a f228 4b40 a5e1 b8989a1904f2 1794141793197

Za a bude taron ƙasa da ƙasa karo na 31 na ƙungiyoyin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi (COP31) a ranar Litinin a birnin Antalya da ke yankin tekun Bahar Rum a Turkiyya.

Taron zai haɗa shugabannin ƙasashe duniya da manyan jami’an gwamnati da masana ilimi da kuma wakilan ƙungiyoyin fararen hula daga sassan daban-daban na duniya.

An soma gudanar da taron ne a birnin Berlin na kasar Jamus a shekarar 1995, kazalika taron na shekara-shekara na ba ƙasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar damar duba irin ci gaban da aka samu wajen yaƙi da sauyin yanayi, da samar da hanyoyin magance matsalolin da suka shafi yanayi tare da cim ma matsaya kan manufofin da za su tsara harkokin sauyin yanayi a duniya.

A bana Turkiyya ce za ta jagoranci taron, wanda zai gudana daga 9 zuwa 20 ga watan Nuwamnba, inda za a tattaun a muhimman batutuwan da suka shafi ci gaba mai ɗorewa da manufofin sauyin yanayi.

An tanadi fili mai girman murabba’in mita miliyan 1.1 a Antalya domin gudanar da COP31, wanda aka tsara a ƙarƙashin taken “COP na Gaba – COP na Aiwatarwa”, wanda aka gina bisa ginshiƙai uku: tattaunawa, cim ma matsaya da kuma ɗaukar mataki.

Taron ya ƙuduri aniyar ƙarfafa aminci da haɗin gwiwa tsakanin ƙasashe, tare da inganta ɗaukar nauyin yaƙi da sauyin yanayi tare, da kuma mayar da alkawuran da aka ɗauka zuwa matakai na zahiri da za a iya tantance sakamakonsu.

Za a gudanar da shirye-shiryen taron a yankuna biyu da aka ware, wato Blue Zone da kuma Green Zone.

Blue Zone zai karɓi manyan tarurruka

Za a gudanar da muhimman yarjejeniyoyi ƙarƙashin tsarin Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi da tattaunawar diflomasiyya a wannan yankin na Blue Zone, inda za a kayyade shiga wurin sai dai da izinin MDD.

Yankin zai kuma gudanar wasu shirye-shirye a gefen babban taron wadanda suka haɗa da tattaunawa kan hanyoyin daidaitawa da sauyin yanayi, da makamashi mai tsafta, da kawar da shara, birane masu ɗorewa, da kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi, da fasaha, lafiya da sauye-sauyen tattalin arziki har zuwa ga kan tsarin da ba ya cutar da muhalli.

Kazalika yankin ya kuma ƙunshi manyan ɗakunan taro, da ofisoshin tawagar ƙasashe daban-daban, da rumfunan baje kolin kayayyaki, da cibiyar ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai, da kuma wuraren cin abinci.

Sannan an ware wani wuri mai siffar fure da ya kai faɗin murabba’in mita 10,000, wanda aka kira “Time Tunnel”, kuma zai kasance gidan tarihi na kawar da shara.

Yankin Green Zone zai ƙunshi cibiyoyi tattaunawa kan muhalli

Yankin Green Zone, wanda aka tsara domin ƙarfafa shigar jama’a cikin harkokin kare muhalli, zai ƙunshi cibiyoyi daban-daban da za su bai wa hukumomin gwamnati, da ‘yan kasuwa, da masana ilimi, da ƙungiyoyin fararen hula da matasa damar musayar dabaru, da fasahohi da kumamuhimman hanyoyin magance matsalolin sauyin yanayi.

Za a yi nune-nune da ka kaɗa-kaɗa, muhawara da bitocin jama’a a wurin.

A wani ɓangare na shirin Zero Waste Movement (Yunkurin Kawar da Shara), wanda ya bazu a duniya, za a samar da cibiyar Zero Waste, wato wata cibiyar koyarwa da kuma yin bitoci kan kawar da shara, da dafa abinci bisa al’adar yankuna bakwai, da wuraren dafa abinci da babu shara da kuma cibiyar wucin gadi ta tattarawa da kuma sarrafa shara zuwa takin zamani.

Haka kuma Green Zone din zai kuma ƙunshi “Antalya House”, wanda zai nuna al’adun gargajiyar na Yörük, da kuma wata rufa ta kunkuru da aka gina da kayayyakin da ba sa haifar da shara.

An sanya wa ɗakunan taro a wurin da sunayen tarihi da al’adun Turkiyya

An sanya wa ɗakunan taro da zauren taruka a cibiyar COP31 da sunayen wuraren tarihi, da fitattun mutane da abubuwan al’adu da ke nuna tarihin Anatoliya da wayewar Turkiyya da Musulunci.

Kazalika an sanya wa babban zauren taro a Blue Zone, wanda zai iya ɗaukar mutane 1,794, suna da “Anadolu”.

Za a yi amfani da wuri wajen karɓar wakilan gwamnatoci da kuma gudanar da yarjejeniyoyi a hukumance.

Haka kuma an sanya wa wani zauren taron mai ɗaukar mutane 828 suna da”Akdeniz”, yayin da akwai wani zauren mai suna Antalya Hall.

An sanya wa ɗaya daga cikin ɗakunan taron manema labarai biyu da ke wurin sunan shahararren malamin sufi kuma mawaƙi, Mevlana Rumi, yayin da ɗayan ke ɗauke da sunan fitaccen mawaƙi kuma malamin falsafa na Turkiyya, Yunus Emre.

Sauran ɗakunan taro a wurin sun haɗa da Selimiye, da Evliya Çelebi, da Ayder, da Göbeklitepe, da Topkapı, da Kaçkar, da Zeugma, da Cappadocia, da Bosphorus, da Patara, da Sümela, da Sezai Karakoç, da Piri Reis, da Harput, da Mimar Sinan, da Dutsen Ağrı, da Tafkin Van, da Troy, da Fethiye, da Pamukkale, da Ephesus, da Gallipoli, da Ahlat, da Uludağ, da Çatalhöyük da kuma Aspendos.

Haka kuma, daga gefe an sanya wa wasu wuraren gudanar da tarukan sunaye kamar Uzungöl, da Lycia, da Assos, da Perge, da Ahi Evran, da Âşık Veysel da kuma Hattusa.

Sannan Blue Zone ya kuma ƙunshi wani lambu na malam buɗe littafi na yankuna masu yanayin zafi, inda baƙi za su samu damar ƙara fahimtar muhalli, da tsarin halittu da kuma bambancin halittun duniya ta hanyar shirye-shiryen da aka tanadar.

A yankin Green Zone kuma, an sanya wa babban zauren da zai iya ɗaukar mutane 5,000 suna da “Gaza Hall”.

Yayin da aka sanya wa sauran ɗakunan taro da wuraren ganawa da sunayen fitattun mutane a tarihi da al’adu, ciki har da Ibn Sina, wanda ya lashe kyautar Nobel Aziz Sancar, da Al-Farabi, da Mehmet Akif Ersoy, da Hacı Bektaş Veli, da Cacabey, daAhmad Yasawi, da Afet İnan, da Fatma Aliye, da Al-Biruni da kuma Osman Hamdi Bey.

The Green Zone’s “Anatolian Garden” will showcase the region’s sheritage, from the Hittites, Phrygians, Lydians, and Lycians to the Roman, Byzantine, Seljuk, and Ottoman periods, emphasising harmony with nature, hospitality, and sustainable living.

“Anatolian Garden”, wato Lambun Anatoliya da ke Yankin Green Zone, zai baje kolin tarihin yankin tun daga zamanin Hittites, Phrygians, Lydians da Lycians, zuwa zamanin daular Roma, Byzantine, Seljuk da Ottoman.

Za a kuma nuna yadda waɗannan al’ummomi suka zauna cikin jituwa da muhalli, tare da al’adun karɓar baƙi da rayuwa mai ɗorewa.

A ƙarƙashin tsarin “Yankuna Bakwai, da Nau’o’in Abinci Bakwai”, taron COP31 zai kuma gabatar wa baƙi da al’adun abinci na Anatoliya, da nau’o’in abincin gargajiya da hanyoyin samar da abinci masu kare muhalli.

Baƙi za su samu damar sanin abincin yankunan Bahar Rum, da Gaziantep, da Kayseri, da Zero Waste, da na duniyar Turkawa, da Konya da kuma na yankin Bahar Maliya.

An tanadi Motoci 630 mara gurɓatar muhalli da za su yi jigilar mahalarta

An tanadi cibiyar kula da yanayin gaggawa a Green Zone ƙarƙashin jagorancin ofishin gwamnan lardin Antalya.

Cibiyar za ta hada wakilan rundunar ‘yansanda ta lardin, da hukumomin lafiya, da hukumar kula da bala’o’i da yanayin gaggawa, da hukumar kashe gobara, da ta kula da ruwa da magudanan ruwa ta Antalya, da kamfanin rarraba wutar lantarki AKEDAŞ da kuma na iskar gas na ENERYA.

Domin tabbatar da samun kulawar lafiya cikin gaggawa, an tanadi cibiyoyin kula da lafiya guda biyar a harabar taron, uku a Yankin Blue Zone, yayin da biyu kuma suke a Yankin Green Zone.

Haka kuma, an shirya motocin agajin gaggawa guda bakwai da wasu biyu da aka ajiye na ko-ta-kwana, yayin da aka jibge ƙungiyoyin agajin gaggawa na likitoci ta ƙasa guda 20, tara a Yankin Blue Zone, 11 a Yankin Green Zone wadanda duk za su ƙarfafa ayyukan ceto.

Haka kuma za a jibge jami’an tsaro 27,957 daga rundunonin ‘yan sanda, jandarma da masu gadin bakin teku domin tabbatar da tsaro a lokacin taron.

Dangane da sufuri kuwa, an tanadi motoci 630 masu amfani da fasahar rage hayaƙin da ke gurɓata muhalli, waɗanda ƙananan hukumomi 25 suka samar, za su riƙa jigilar mahalarta taron.