‘Yansandan Nijeriya 10 sun rasa rayukansu a musayar wuta da mahara a arewacin ƙasar, in ji hukumomi

Wata mummunar musayar wuta tsakanin wasu mahara da ke ɗauke da makamai da jami’an tsaron Nijeriya ta yi sanadiyyar mutuwar jami’ai 10 da mahara 17 a wani ƙauye a Masarautar Zuru a kan iyakar jihohin Kebbi da Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar.

Newstimehub

Newstimehub

11 Aug, 2026

7441bc24 dcc7 461b 9c10 26a8739b6207 1786467064438

Wata mummunar musayar wuta tsakanin wasau mahara da ke ɗauke da makamai da jami’an tsaron Nijeriya ta yi sanadiyyar mutuwar ‘yansanda 10 a yanki mai nisa da ke arewacin ƙasar, in ji rundunar ‘yansandan Jihar Kebbi a ranar Talata.

Arangamar, wadda ta afku a ranar Litinin a yankin ƙaramar Hukumar Sakaba da ke Masarautar Zuru a jihar ta Kebbi, ta kuma janyo mutuwar fararen hula biyu da mahara 17, in ji kakakin ‘yansandan Jihar ta Kebbi Bashir Usman a wata sanarwa da ya fitar.

Har yanzu ba a san su waye maharan ba a yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin, in ji ‘yansanda.

Kakain ‘yansandan ya ce maharan sun far wa ƙauyen Makuku ne a Masarautar Zuru da ka kan iyakar Kebbi da Zamfara da nufin kai wa mazauna garin hari, da kuma yiwuwar yin garkuwa da wasusnsu.

Usman ya ce nan da nan jami’an ‘yansandan kwantar da tarzoma suka isa yankin, inda suka yi mummunar musayar wuta da ‘yanta’addan.

Jami’in ‘yansadan ya ce an kashe 17 daga maharan, sannan da dama sun gudu da raunin bindiga.