Hukumomi a ƙasar Uganda sun kama sama da mutane 200 ’yan ƙasashen waje a wani sabon samame da aka gudanar domin dakile hijira ba bisa ka’ida ba da kuma yiwuwar aikata laifuka. An gudanar da wannan samame ne a arewacin ƙasar da kuma babban birni, Kampala, inda jami’ai suka ce an gano mutane da dama ba tare da takardun shaida ba.
Rahotanni sun nuna cewa da yawa daga cikin waɗanda aka kama ba su da fasfo ko katin shaida, kuma suna rayuwa ne a wurare da ake takaita musu zirga-zirga. A wasu lokuta, an same su a cikin wani katafaren wuri da ba a yarda su shiga ko fita yadda suka ga dama ba, duk da cewa akwai wasu kayan more rayuwa kamar wurin cin abinci da na nishadi.
Mai magana da yawun shige da fice, Simon Peter Mundeyi, ya bayyana cewa ana zargin an shigo da su ƙasar ne da alkawarin samun ayyukan yi, amma daga bisani aka kwace takardunsu tare da ware su zuwa rukuni-rukuni. Gwamnati na kuma zargin akwai alaƙa da safarar mutane da damfara ta yanar gizo, inda ake ci gaba da bincike domin gano waɗanda ke da hannu a lamarin.
Jami’ai sun ce mutanen da aka tsare sun kasu gida uku: wasu na iya zama waɗanda aka yi safararsu, wasu kuma ana zargin suna da hannu a ayyukan ba bisa ka’ida ba, yayin da wasu kawai suka wuce wa’adin zaman visa dinsu.
Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB














