Shugaban Senegal Faye ya sallami Firaministansa Ousmane Sonko

Ousmane Sonko ne babban ɗan adawan tsohon Shugaban Senegal Macky Sall, an hana Sonko tsayawa takarar shugabancin Senegal wanda hakan ya sa ya goyibayan Shugaba Bassirou Faye.

Newstimehub

Newstimehub

23 May, 2026

724fa0ac93ac3190c743cfbd543d4fa5cedab00200a66c91972df0cd122bd2d2

Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya sallami Firaministansa kuma tsohon mai ba shi shawara, Ousmane Sonko, a ranar Jumma’a da dare..

A cewar wata sanarwa da sakatare janar na fadar shugaban kasa, Oumar Samba Ba, ya karanta a gidan talabijin na ƙasa, shugaban ya kori Mista Ousmane Sonko, Firaminista, da ministocinsa da sakatarori da sauran ma’aikatan da ke ƙarƙashin gwamnatinsa.

“Alhamdoulillah. A daren yau zan yi bacci da zuciya cikin sauƙi a unguwar Keur Gorgui,” in ji Sonko nan take a shafin Facebook dinsa. Keur Gorgui unguwa ce a Dakar inda gidansa yake.

A matsayin abokin adawa na tsohon shugaban ƙasa Macky Sall (2012-2024), an hana Sonko damar tsayawa takarar shugabancin ƙasa a 2024 kuma ya goyi bayan takarar Faye.