Shugaban South Africa Cyril Ramaphosa ya dakatar da babban jami’in ‘yan sanda Fannie Masemola saboda zargin da ake masa a kotu.
Ana zargin Masemola da gazawa wajen sa ido kan wata kwangilar lafiya mai darajar dala miliyan 21, wadda yanzu ake bincike a kai kuma an soke ta.
Shi dai ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa ba shi da laifi, amma ya amince a bar doka ta yi aikinta.
Ramaphosa ya ce ya ɗauki matakin ne saboda muhimmancin mukamin da kuma buƙatar tabbatar da sahihanci da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro.
Za a ci gaba da dakatar da shi har sai an kammala shari’ar da ake yi a kansa.
Tushen labari: Newstimehub














