Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin N60m kan kwamandan ISWAP da mataimakinsa

Rundunar ta ce za ta ba da naira miliyan 50 ga duk wanda ya samar mata bayanai da za su kai ga kama kwamandan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP, Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa.

Newstimehub

Newstimehub

6 Aug, 2026

af8ec202 b056 4536 afeb 991c4140f945 1786004101665

Rundunar sojin Nijeriya ta sanya tukuicin Naira miliyan 60 ga duk wanda ya samar mata da bayani kan yadda za ta kama kwamandan ƙungiyar ISWAP a Yammacin Afirka da mataimakinsa da ake nemansu ruwa-a-jallo a yankin Tafkin Chadi.

Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da muƙaddashin mai magana da yawun rundunar Operation Hadin Kai na yankin Maiduguri, Kyaftin Mohammed Goni ya fitar ranar Laraba.

Rundunar ta ce za ta ba da naira miliyan 50 ga duk wanda ya bayar da bayanai da za su kai ga kama kwamandan ƙungiyar ta’addanci ta ISWAP, Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa, yayin da shi kuma mataimakinsa, Muhammad Jidda aka sanya tukuicin naira miliyan 10 ga duk wanda ya samo bayanai akansa.

Ta ƙara da cewa tana neman bayanai kan yadda za ta kama Hamad Abu Hanifa, wani babban jami’in ƙungiyar ta ta’addanci.

Sanarwar ta ce an gano waɗanda ake nema ruwa-a-jallon ne ta hanyar binciken ƙwaƙwaf daga na’urorin leƙen asiri da aka samu a lokacin samamen da dakarun rundunar Operation Haɗin Kai suka kai kwanan nan a jihar Borno da ke yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.

Daga cikin kayayyakin da aka ƙwato, har da kyamara da ake zargin an yi amfani da ita wajen ɗaukar bidiyoyin farfaganda, wadda ta taimaka wajen gane fuskoki da kuma wuraren da manyan jami’an ISWAP ke aiki a yankin Mangari-Metele-Dogon Chukun da ke kusa da Tafkin Chadi, a cewar sanarwar.

Rundunar sojin ta buƙaci jama’a da su samar da bayanai masu inganci da za su iya kaiwa ga kama waɗanda ake zargin, sannan ta yi alƙawarin kare sirrin waɗanda suka samar mata da bayanan.