Nijar da wani kamfani sun ƙulla yarjejeniyar gina matata mai tace gangar mai 100,000 a yini

Ya ƙara da cewa matatar za ta kawo ƙarshen dogaron Nijar kan mai daga ƙetare, yana mai ƙarawa da cewa abin da Nijar ba ta sha ba daga man za a fitar da shi ƙasashe maƙwabta a yankin.

Newstimehub

Newstimehub

16 Aug, 2026

ee68fb59 868d 45c9 944a d66917c471c9 1786868381504

Gwamnatin Nijar da kamfanin Zimar Group da High Tech sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyar gina matatar mai wadda za ta iya tace gangar mai 100,000 a ko wace rana kan kuɗi dala biliyan $1.9.

Matatar mai ɗin da za a gina a Dosso cikin Jamhuriyar Nijar za a gina ta ne cikin shekaru uku kuma kamfanin zai tafiyar da ita na shekara 13 kafin ya miƙa ta ga gwamnatin Nijar.

Ranar Asabar ne shugaban kwamitin da ke wakiltar Nijar wajen yarjejeniya kan batun mai Bakary Yaou Sangarékan da shugaban kamfanin Zimar Group da High Tech, Mista Benjamin Day Marc suka rattaba hannu a kan yarjejeniyar,” in ji kamfanin dillancin labaran Nijar (ANP).

Kamfanin dillancin labaran ya ambato shugaban kwamitin yana cewa “domin tabbatar da cewa an aiwatar da aikin yadda ya kamata da kuma kare haƙƙin ƙasa, an saka wa aikin wa’adi.” 

Kamfanin da zai gina matatar yana da watanni huɗu domin samo kuɗaɗe da kuma samar da cikakken bayanan aikin tare da tabbatar da cewa ya kammala duk lamari na kuɗi cikin watanni 12, in ji rahoton na ANP.

“Waɗannan muhimman matakan za su ba dama ga kwamitin sa ido kan aiwatar da aikin ya bibiyi yadda abokin aikin [kamfanin] ke aiwatar alƙawurransa da kuma tabbatar da cewa aikin ya ci gaba cikin wani bayyanannen tsari da ya dace da muradun ƙasa,” kamar yadda ANP ya ambato Bakary Yaou Sangaré yana cewa. 

“Yarjejeniyar da aka miƙa domin rattaɓa hannu tsakanin jamhuriyar Nijar da Zimar Group ta ƙunshi tsara da ɗaukar nauyi da gina da jagoranta da kuma miƙa matatar mai mai iya tace gangar mai 100,000 a ko wace ranar, tare da wani wajen sarrafa man fetur da sinadirai a Dosso,” kamar yadda shugaban kwamitin ya bayyana.

“Aikin ya biyo bayan Yarjejeniyar Fahimtar Juna da aka rattaɓa hannu a kan sa ne a watan Oktoban shekarar 2024, wadda ta sa aka fara tattaunawa da kamfanoni da suka haɗa da Zimar Group, wani kamfamin da aka kafa a ƙarƙashin dokar Nijar da kuma Hightech, wani kamfanin Amurka, wanda ya samar da yarjejeniyar aikin tsakanin gwmanati da ‘yankasuwa da aka miƙa don rattaɓa hannu a kai yau,” in ji Bakary Yaou.

Ya ce rattaɓa hannu kan yarjejeniyar wani muhimmin mataki ne da ke nuna jajircewra Nijar wajen faɗaɗa abokanan cinikayyana da ƙara sarrafa albarkatun dake cikin ƙasarta da kuma ƙara ƙarfafa ƙarfinta na masana’antu da ƙarin ƙima da buɗe sabbin damarmaki ga ƙasar, in ji Bakary Yaou Sangaré.

Shi kuma shugaban kamfanin Zimar Group, Mista Benjamin Day Marc, ya ce kamfanin zai gina wata matata ta zamani da ke mutunta ƙa’idoji na kariya [gamutane] da kiyaye muhalli na ƙasashen duniya a Dosso.

Ya ce kamfanin zai samar da kayayyaki da ke da nasaba da matatar ciki har da bututun mai da rumbun ajiya da sauran kafofin masana’antu masu alaƙa lamarin da zai samar da dubban ayyukanyi ga matasan Nijar da kuma ba da ilimi da ƙwarewa ga ‘yan ƙasar.

“Ƙwararrunmu na ƙetare ba wai kawai suna tahowa Nijar ba ne domin aiki. Suna tahowa domin horas da ko wane injiniya da mai fasaha da ma’aikaci kuma za su miƙa ƙwarewarsu ga abokanan aikinsu ‘yan Nijar saboda a lokacin da aka miƙa wannan aikin ga ƙasar, mata da maza da za su yi aiki a cikinsa za su kasance ‘yan Nijar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa matatar za ta kawo ƙarshen dogaron Nijar kan mai daga ƙetare, yana mai ƙarawa da cewa abin da Nijar ba ta sha ba daga man za a fitar da shi ƙasashe maƙwabta a yankin.

“Ga ƙasar da ba ta da teku, ‘yancin kai na makamashi ba kawai take ba ne, amma batu ne na tsaro,” kamar yadda ANP ta ambato shugaban na Zimar yana cewa.