Tsohon Shugaban kamfanin mai na ƙasa na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya yi watsi da zarge-zargen sani wani abu game da kuɗi naira tiriliya ₦210 da majalisar dattawa ta ce ba a san yadda aka yi da su ba, yana mai cewa babu kuɗin da aka rasa a ƙarƙshin kulawarsa.
Kyari ya ce zarge-zarge masu alaƙa da bayanan kuɗin kamfanin tsakanin 2017 da 2023 an yi su ne bisa kura-kurai wajen shigar da bayanai da kuma matsalolin lissafi.
Ya yi bayanin ne ranar Talata a lokacin da ya bayyana a gaban kwamiti na majalisar dattawa kan Lissafin kudin gwamnati, wanda ke bincike kan tambayoyin da ofishin Babban Mai Binciken Kudi na Tarayyar Nijeriya ya yi game da bayanan kuɗin NNPCL a cikin lokacin.
Da yake bayani game da lamarin, Kyari ya ce kamfanin ya yi ƙoƙarin aiwatar da ƙudurorin Majalisar Dokoki ƙasar, lamarin da ya janyo zuba jari mai ɗorewa da inganta fannin tace mai domin amfanin ƙasar.
“Ina alfaharin cewa mun yi wa wannan ƙasa hidima a hanya mafi dacewa. Ina biyayya ga wannan ƙasa kuma ban yi wani abun da ba daidai ba da gangan,” in ji shi.
Kan kuɗaɗen da aka biya Hukumar Tara Haraji Ta Tarayya (FIRS), Kyari ya ce kuɗaɗen na rijista ne, yana mai bayyana rashin daidaiton a matsayin matsalolin shigar da bayanai. Ya kuma ce naira biliyan ₦2.9 da ake magana a kai kuɗaɗen da doka ta tanadi biyansu ne.
Da yake magana game da zargin naira biliyan ₦5 da aka ce an kashe kan sake yi wa NNPCL suna, tsohon shugaban kamfanin ya ce Majalisar Dokokin ce ta sauya sunan, yana mai cewa ba a biya ko wane kuɗi ba kan sauyin.
Daga bisani Kyari ya gabatar da rahotonsa ga kwamitin.
A nasa martanin, shugaban kwamitin ya ce anyi tambayoyi game da batutuwa 23 a gaban kwamitin, inda ɗaya ko biyu ne kawai ke da alaƙa da tsohon babban jami’in NNPCL ɗin.
Ya ce za a rarraba rahoton tsakanin mambobin kwamitin domin su yi nazari a kai, yana mai ƙarawa da cewa kwamitin zai gayyaci waɗanda lamarin ya shafa da kuma Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya, domin ƙarin haske idan buƙatar hakan ta taso.
“Mun karɓi haƙurin da ka bayar bisa rashin bayyanarka a zaman kwamitin na baya kuma za mu yi nazari bisa alƙalluman,” in ji shugaban kwamitin.
Daga bayan kwamitin ya sallami Kyari zuwa ƙarshen bincikensa.
Kwamitin Majalisar Dattawa kan Kuɗin Gwamnati ya fara binciken alƙalluma da ake ce-ce-ku-ce a kai ne a watan Yunin shekarar 2025 bayan an bayyana saɓani a bayanan kuɗin NNPCL daga shekarar 2017 zuwa 2023.
Alƙalumman sun haɗa da naira tiriliyan ₦103 a matsayin kuɗaɗen da aka tara da kuma naira tiriliyan ₦107 da ba sa cikin kuɗaɗen shiga na yau da kullum. Kwamitin ya daɗe yana watsi da bayanan da kamfanin ya bayar, yana mai cewa dole a yi bayanin yadda aka shigar da bayanan.
A watan Maris na shekarar 2026, kwamitin ya yi wa Kyari da sauran tsaffin ma’aikatan kamfanin sammaci domin bayanai game da alƙalluman. Daga baya ya ba da umarnin kama shi a watan Yuni bayan ya gaza bayyana a gabansa. Sai dai kuma tsaffin jami’an NNPCL sun musanta cewa kuɗin ya ɓace, suna masu cewa naira tiriliyan ₦210 ɗin ya fito ne daga rashin bayyana bayanan kuɗin kamfanin yadda ya kamata.















