Jaridar Financial Times ta rawaito a ranar Laraba cewa, Iran na duba yiwuwar kai gagarumin hari kan kadarorin sojojin Amurka a Turai idan Shugaba Donald Trump ya ƙara ƙaimi a yaƙin da suke gwabzawa, yayin da Tehran ke neman faɗaɗa rikicin fiye da Gabas ta Tsakiya.
Da take ambato wasu mutane biyu da ke kusa da gwamnatin Tehran, jaridar ta Birtaniya ta ce sojojin Iran sun tabbatar da yiwuwar kai hari kan cibiyoyin Amurka a ƙasashen kudu maso gabashin Turai, ciki har da Bulgaria, wadda a watan da ya gabata ta amince Amurka ta yi amfani da sansanin sojin samanta na Bezmer don kai hari Iran.
Kudancin Cyprus da ke ƙarƙashin ikon Girka, inda wani jirgi maras matuƙi ya faɗa kan sansanin sojin saman Birtaniya a watan Maris, na daga cikin waɗanda za a iya kai wa hari idan Amurka ta sake kai hari Iran, a cewar ɗaya daga cikin majiyoyin.
Rundunar sojojin Iran ta yi nazari daban-daban kan yiwuwar kai hari kan wayoyin sadarwa na ƙarƙashin teku a Mashigar Hormuz idan aka ƙara kai mata hari.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Financial Times cewa Tehran na shirin faɗaɗa rikicin idan Trump ya aiwatar da barazanar da ya yi a baya bayan nan ta kai hari kan kayayyakin more rayuwa na Iran.
“Idan Amurka ta yi nisa sosai, Iran za ta kare kanta a kowane yanayi, ta wuce yankin ta kuma kai hari kan Turai ma,” in ji majiyar.
Rahoton ya zo ne yayin da tattaunawa kan sake buɗe Mashigar ruwa ta Hormuz ta tsaya cak kuma hasashen sake buɗe mashigar ruwan daga Tehran da Washington ya ragu.
Trump a ranar Talata ya bayyana cewa babu “wata tattaunawa ko ganawa da ake yi, ko aka tsara yi” da Tehran.
Jami’an sojin Iran sun yi gargaɗin cewa duk wani sansanin soja da ake amfani da shi don kai hare-hare kan yankin Iran za a iya ɗaukar sa a matsayin wajen kai hari.
Rahoton ya kuma ambaci ƙwararrun sojoji suna cewa Iran tana da makamai masu linzami da za su iya isa sassan kudu da kudu maso gabashin Turai, ko da yake ingancinsu da daidaitonsu na iya raguwa a tsawon lokaci.
Iran da Amurka sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a watan Yuni da nufin kawo ƙarshen yaƙin da kuma shimfiɗa hanya ga wata yarjejeniya mai faɗi, amma daga baya yarjejeniyar ta wargaje sakamakon zargin juna da keta haddi da kuma sake ɓarkewar rikici.
Tun daga lokacin, ƙoƙarin diflomasiyya ya gaza samar da wani ci-gaba kan sake buɗe mashigar ruwa ta Hormuz ko kuma sake fara tattaunawa kan wata yarjejeniyar mai faɗi.















