Kasashen Turkiyya, Saudiyya da Pakistan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa, wadda ta tanadi cewa duk wani hari da makamai da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen uku za a dauke shi a matsayin hari da aka kai wa dukkansu, kamar yadda sanarwar haɗin gwiwa da aka fitar a ranar Juma’a ta bayyana.
An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Makka, inda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman, da Firaministan Pakistan Shehbaz Sharif suka halarci wani taro wanda Saudiyya ta shirya a hukumance.
Sanarwar haɗin gwiwar ta ce yarjejeniyar ta samo asali ne daga “kyakkyawar alakar tarihi, ‘yan’uwantaka mai daɗaɗɗen tarihi, haɗin kan Musulunci, muradun tsaro da dabarun bai ɗaya, da kuma haɗin gwiwar tsaro da aka daɗe ana yi” tsakanin ƙasashen uku.
Yarjejeniyar na da nufin ƙara ƙarfin daƙile duk wani hari daga makiya, tare da faɗada haɗin gwiwar tsaro a dukkan fannoni.
Shugabannin ƙasashen sun ce yarjejeniyar na nuna aniyarsu ta bai ɗaya wajen inganta tsaron gama gari, bunƙasa zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali a yankin da ma duniya baki daya, tare da gina makoma mai aminci da wadata.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Pakistan ta sake jaddada cewa yarjejeniyar ta tanadi cewa “duk wani hari da makamai da aka kai wa ɗaya daga cikin ƙasashen uku za a ɗauke shi a matsayin hari da aka kai wa dukkansu.”
Ta ce manufar yarjejeniyar ita ce ƙara karfin hadin gwiwar tsaro da dabarun yaki tsakanin kasashen uku domin dakile duk wani hari.
Shugabannin sun gana a Makka
Tun da farko a ranar Juma’a, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya Mohammed bin Salman a Fadar Al-Safa da ke Makka, a yayin ziyarar aiki da yake yi a Saudiyya.
A cewar sanarwar hadin gwiwa, shugabannin sun tattauna kan kyakkyawar alakar kasashen Saudiyya, Turkiyya da Pakistan, da kuma batutuwan da suka shafi muradun ƙasashen.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa Ibrahim Kalin, jakadan Turkiyya a Riyadh Emrullah Isler, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Hasan Dogan su ma sun halarci taron.
Yarjejeniyar ta zo ne a lokacin tashin hankali a yankin
An cim ma yarjejeniyar ta Makka ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarin tashin hankali a yankin, bayan ɓarkewar yaƙin da Amurka ta fara da Iran a ranar 28 ga Fabrairu na wannan shekara.
Tun daga lokacin, Saudiyya ta fuskanci ɗaya daga cikin manyan hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa mafi muni a tarihinta na baya-bayan nan, inda Iran ta riƙa kai hare-hare kan sansanonin soji, cibiyoyin makamashi da wuraren fararen-hula.
A cewar mahukuntan Saudiyya, zuwa ranar 7 ga Afrilu, Iran ta harba jiragen yaƙi marasa matuƙi 1,131 da makamai masu linzami na ballistic da cruise guda 140 zuwa cikin masarautar, inda aka kai hare-hare kan cibiyoyin mai, tashoshin samar da wutar lantarki, sansanonin soji, wuraren fararen-hula da kuma ofisoshin jakadancin ƙasashen waje.
Rikicin ya kuma bazu zuwa wajen iyakokin Iran, inda mayaƙan Houthi masu goyon bayan Iran suka ƙara kai hare-hare kan jiragen ruwan Saudiyya a Tekun Bahar Maliya.
Taɓarɓarewar yanayin tsaro a yankin ta ƙara hanzarta haɗin gwiwar tsaro tsakanin ƙasashen yankin. A shekarar 2025, Saudiyya da Pakistan sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsaro ta ƙasashen biyu, wadda ta ja hankalin duniya saboda Pakistan ita ce kaɗai ƙasa mai rinjayen Musulmi da ke da makamin nukiliya.














