Biranen Afirka 25 da Amurka za ta rufe ayyukan bayar da biza daga ranar 1 ga Agustan 2026

A tsakiyar watan Yulin 2026, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da dakatar da bayar da biza daga birane 25 a faɗin Afirka, inda tilas masu neman bizar su tafi wasu biranen a abin da Washington ta bayyana “cibiyoyin yanki.”

Newstimehub

Newstimehub

30 Jul, 2026

dace2f0a 9871 4ceb 9e78 aeccb8f022db 1785350261057 main

A tsakiyar watan Yulin 2026, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da dakatar da bayar da biza daga birane 25 a faɗin Afirka, inda tilas masu neman bizar su tafi wasu biranen a abin da Washington ta bayyana “cibiyoyin yanki.”

A sanarwar da Ma’aikatar ta wallafa a ranar 15 ga Yuli, ta ce: “Daga 1 ga Agustan 2026, Ma’aikatar Harkokin Wajen za ta sake daidaita ayyukan biza na yau da kullum a cikin biranen da aka ambata guda 25.”

Biranen da abin ya shafa sune: Antananarivo (Madagascar), Abuja (Niijeriya), Asmara (Eritrea), Bamako (Mali), Banjul (Gambia), Brazzaville (Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo), Bujumbura (Burundi), Conakry (Guinea), Cotonou (Benin), Durban (Afirka ta Kudu), Freetown (Sierra Leone), Gaborone (Botswana), Harare (Zimbabwe), Juba (Sudan ta Kudu), Libreville (Gabon), Lilongwe (Malawi), Lusaka (Zambia), Maputo (Mozambique), Maseru (Lesotho), Mbabane (Eswatini), N’Djamena (Chadi), Yamai (Nijar), Nouakchott (Murtaniya), Ouagadougou (Burkina Faso), da Windhoek (Namibiya).

Masu neman biza, waɗanda a da za su shigar da buƙat izinin shiga a ofisoshin jakadanci ko ƙananan ofisoshin jakadancin Amurka a waɗannan biranen, yanzu tilas su tafi wasu biranen, ko ma wasu ƙasashe, domin ganawar neman biza.

Bisa ga sharuɗɗan Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, TRT Afrika ta tattara sabbin cibiyoyin neman biza ga mutanen da abin ya shafa. Ga bayanan biranen da abin ya shafa da kuma sabbin biranen da za su maye gurbinsu a gabansu:

Antananarivo (Madagascar) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Abuja (Nijeriya) — Legas (Nijeriya)

Asmara (Eritrea) — Kampala (Uganda)

Bamako (Mali) — Dakar (Senegal)

Banjul (Gambia) — Dakar (Senegal)

Brazzaville (Jamhuriyar Kongo) — Kinshasa (Kongo DRC)

Bujumbura (Burundi) — Kampala (Uganda)

Conakry (Guinea) — Dakar (Senegal)

Cotonou (Benin) — Lome (Togo)

Durban (Afirka ta Kudu) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Freetown (Saliyo) — Monrovia (Laberiya)

Gaborone (Botswana) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Harare (Zimbabwe) — Johannesburg, Cape Town (Afirka ta Kudu)

Juba (South Sudan) — Kampala (Uganda)

Libreville (Gabon) — Yaounde (Kamaru)

Lilongwe (Malawi) — Nairobi (Kenya)

Lusaka (Zambia) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Maputo (Mozambique) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Maseru (Lesotho) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

Mbabane (Eswatini) — Johannesburg (Afirka ta Kudu)

N’Djamena (Chadi) — Yaounde (Kamaru)

Yamai (Nijar) — Lome (Togo)

Nouakchott (Mauritania) — Dakar (Senegal)

Ouagadougou (Burkina Faso) — Lome (Togo)

Windhoek (Namibia) — Johannesburg, Cape Town (Afirka ta Kudu)

Ma’aikatar ta ce: “‘Yanƙasa da mazauna waɗannan ƙasashe da suke son neman bizar Amurka a ranar ko kafin 1 ga Agustan 2026, dole ne su nemi lokacin da za a gana da su, kuma su biya kuɗin biza da ake buƙata a wuraren bizar da aka tsara.”

Sauran ayyukan ofisoshin jakadancin da ƙananan ofisoshin jakadancin za su ci gaba

Washington ta ce ta daidaita ayyukan bizar ne a Afirka da wasu yankuna na duniya a matsayin “wani ɓangare na dogon tsarin Ma’aikatar wanda ke ƙarfafa tsaron ƙasa ta hanyar inganta daidaitattun matakan bincike, da antancewa, da yanke hukunci, da kuma inganta ayyuka.”