Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin motoci da sojoji ke rakiya a arewacin Ghana, inda mutane uku suka mutu, daya kuma ya jikkata. Ayarin, wanda ke ɗauke da fararen hula kusan 140, na kan hanyarsa daga Bawku zuwa Bolgatanga ne lokacin da aka buɗe musu wuta kusa da Binduri.
Sojoji sun mayar da martani cikin gaggawa, inda suka fatattaki maharan tare da kashe bakwai daga cikinsu. Haka kuma jami’an tsaro sun kama wasu da ake zargi tare da kwato makamai a yayin aikin.
Wannan hari na daga cikin rikicin da ya dade yana faruwa a yankin Bawku, wanda ke da nasaba da sabanin da ke tsakanin al’ummomin Kusasi da Mamprusi, musamman kan batun sarautar gargajiya. Duk da dokar hana fita, tura sojoji da kuma yunƙurin sasanci, rikicin na ci gaba da jawo hare-hare da ramuwar gayya, yana kawo cikas ga rayuwar jama’a da kasuwanci.
MAJIYAR LABARI: NEWSTIMEHUB









