Jami’an Hukumar EFCC sun karɓe wani gida mallakin tsohon minista Abubakar Malami a Abuja, bisa umarnin kotu da hukumar ta ce ya samu cikakken tushe daga doka. An girke jami’an tsaro masu yawa a yankin, lamarin da ya hana mazauna da baƙi shiga titin na ɗan lokaci yayin da ake gudanar da aikin.
Hukumar ta jaddada cewa matakin da aka ɗauka ya bi sahihin tsarin shari’a, kuma jami’anta suna aiki ne bisa izinin kotu. Wannan ya biyo bayan wasu ayyuka na baya-bayan nan da hukumomin tsaro suka gudanar kan kadarorin tsohon ministan a sassa daban-daban na Babban Birnin Tarayya.
A ranar Litinin da ta gabata ma, jami’ai sun riga sun sanya alamar kwace gidan, abin da ke nuna cewa ana ci gaba da bincike da matakan doka kan kadarorin da ake zargi.














