Jirgin ƙasan da ke zirga-zriga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Nijeriya ya yi hatsari bayan da ya sauka daga layinsa a ranar Talata.
Lamarin ya faru ne a garin Asham, kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook, Imo Onyekwereya wallafa faruwar lamarin kai-tsaye ta bidiyo a shafinsa.
Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11 na safe, jim kaɗan bayan tashin jirgin daga Abuja zuwa Kaduna.
A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda taragun jirgin suka tuntsura, kuma mutane sun taru a wajen suna kallon abin da ya faru da ƙoƙarin aikin ceto, yayin da wasu da suka fi kama da fasinjoji na tsaye cirko-cirko.