Hukumar ƙwallon ƙafar Turai, UEFA ta nuna wani saƙo a ƙyalle mai alaƙa da yankin Gaza da aka yi wa ƙawanya. Saƙon na cewa: “A Daina Kashe Yara. A Daina Kashe Fararen-hula”, gabannin wasan Super Cup na UEFA tsakanin Paris Saint-Germain da Tottenham.
“Saƙon a bayyane yake ƙarara,” cewar UEFA a shafinta na X ranar Laraba. “Wata bana. Wani kira.”
Gabannin wasan, wasu yara daga wuraren da yaƙe-yaƙe suka shafa sun ɗaga ƙyallen mai rubutu, ciki har da yara biyu daga Gaza.
Lamarin ya biyo bayan sanarwar Gidauniyar Yara ta UEFA mai cewa za ta taimaka wa yara =n da yaƙe-yaƙe suka shafa a yankuna daban-daban na duniya.
Haka nan lamarin ya zo ne bayan sukar da ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya yi wa hukumar UEFA kan mutuwar Suleiman al-Obeid, da aka fi sani da “Pelen Falasɗinawa”, saƙon da bai yi tir ko ambata yadda aka kashe shi a Gaza ba.









