Rundunar ’yansandan Jihar Kogi ta kama wani mutum mai suna Jacob Irewa, mazaunin rukunin gidaje na Oworo da ke Felele a Lokoja, bisa zargin cewa ya zuba wa matarsa, Berida Irawo, fetur sannan ya cinna mata wuta bayan wata takaddama ta cikin gida.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da rana a gidansu, sakamakon wani saɓani da ya shafi ɓacewar rigunan mijin masu gajeren hannu.
An ce rikicin ya fara ne bayan mijin ya gano cewa rigunansa masu gajeren hannu guda bakwai wadanda ya ce yana matuƙar so sun ɓace daga ɗakinsa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
“Na dawo daga waje, na yi wanka, sai na so in saka ɗaya daga cikin rigunan da na fi so, guda bakwai ne, amma ban ga ko ɗaya daga cikinsu a ɗakin ba. Na bincika ko’ina, har da wurin da muke shanya tufafi a kan igiya a bayan gidan domin su bushe,” in ji shi.
Ya ce daga nan ya tambayi matarsa game da rigunan a cikin ɗakin, sai ta fita waje tana gaya masa cewa ta ƙona su, bayan da ya matsa mata da tambayoyi.
Ya ce ya tambaye ta dalilin da ya sa ta ƙona rigunan.
“Saboda takaici da fushi, sai na je inda na ajiye babur dina, na ɗebo fetur daga cikinsa, na zuba mata sannan na cinna mata wuta da ashana. Ban san yadda abin ya faru ba; Allah Ya gafarta mani,” in ji shi.
Wanda ake zargin, wanda ya ce shi limamin coci ne da aka naɗa kuma malami ne a ƙauyen Irawo, ya ce yana hutu ne a Lokoja. Ya kuma bayyana cewa bai taɓa faɗa da matarsa kan wani abu ba.
Ya ce sun shafe shekaru da aure amma ba su samu ɗa ba.
Sai dai Rundunar ’Yansandan Jihar Kogi ta tabbatar da kama shi bisa zargin ƙoƙarin kisan kai da ya shafi matarsa, Berida Irawo.
’Yansandan sun ce sun samu rahoton lamarin ne ranar Jumma’a, 14 ga Agustan 2026, da misalin ƙarfe 8:30 na dare.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta ce binciken farko ya nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga wata taƙaddamar cikin gida, amma matar ta tsira daga harin kuma a halin yanzu tana samun kulawa a asibitin Honey Gold da ke Felele.















