Yadda Super Eagles ta doke Taifa Stars a gasar AFCON

Kungiyar Super Eagles ta Nijeriya ta samu nasara kan takwararta ta Taifa Stars ta Tanzania da ci 2 da 1 a wasan rukunin C na gasar kwallon kafa ta Kasashen Afirka AFCON.

Newstimehub

Newstimehub

24 Dec, 2025

e73e3653677be114ed962808b5893e29287a03e8076f0a8584b7d6aac21cc4b3

Tun da fari, a minti na 36 ne dan wasan Super Eagles Semi Ajayi ya jefa kwallo a ragar Taifa Stars wand aya sanya Nijeriya zama a kan gaba.

Haka aka ci gaba da fafatawa har zuwa karshen zagayen farko na wasan.

Bayan na dawo zagaye na biyu, dan wasan Taifa Stars Charles M’Mombwa ya zura kwallo a ragar Nijeriya wanda ya sanya wasan koma wa sabo, 1 da 1.

Amma cikin hanzari, kasa da mintuna biyu da Tanzania ta farke kwallonta, dan wasan Nijeriya Ademola Lookman ya jefa kwallo ta biyu a ragar Tanzania.

An tashi wasan Nijeriya na da kwallaye biyu, Tanzania kuma na da kwallo daya tilo.

Kungiyar Super Eagles ce ta mamaye zagayen farko na wasan, inda Akor Adams da Victor osimhen suka yi ta kai farmaki.

A rukunin C na gasar ta AFCON 2025 da ake buga wa a kasar Morocco, akwai kasashen Nijeriya, Tunisia, Tanzania da Uganda.