Turkiyya ta kama ɗanta’addan FETO da ake nema bisa ƙoƙarin kashe Shugaba Erdogan a shekarar 2016

Wanda ake zargin, wani keftin na soji da aka kora kuma tsohon matuƙin helikwafta, ya kasance ana nemansa ruwa-a-jallo a ƙarƙashin wata Jar Sanarwar ta Hukumar ‘Yansandan Duniya.

Newstimehub

Newstimehub

1 Aug, 2026

2b8c9553 631d 4380 9f8a cc6eda79fcb0 1785571248015

Rundunar ‘yansandan Turkiyya ta kama wani mamba na ƙungiyar ‘yanta’adda ta FETO wanda ake nema ruwa-a-jallo bisa ƙoƙarin kashe shugaban ƙasar a lokacin ƙoƙarin juyin mulkin da aka ci galaba a kansa a shekarar 2016, in ji ma’aikatar tsaron cikin gidan ƙasar.

Wanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa da harrufan da ke farkon sunayensa BK, ya kasance cikin ɓangare na ƙungiyar ta’addancin FETO da ke da hannu cikin ƙoƙarin kashe Shugaba Recep Tayyip Erdogan a Marmaris yayin yunƙurin juyin mulkin watan Yulin shekarar 2016, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana ranar Asabar.

Ma’aikatar ta ce wanda ake zargin wani keftin na soji ne da aka kora kuma matuƙin helikwafta wanda ake nema ruwa-a-jallo a ƙarƙashin Jar Sanarwar Hukumar ‘Yansandan Duniya.

Ɓangarorin tattara bayanan sirri na ‘yansanda a lardunan Afyonkarahisar da Eskisehir sun ƙaddamar da aiki na haɗin gwiwa da sashen Tattara Bayanan Sirri na Tsaro, in ji ma’aikatar.

Samamen ya gano inda wanda ake zargin, wanda aka bayyana sunansa a matsayin BK, sa’annan ‘yansandan da ke yaƙi da ta’addanci suka kama shi a Afyonkarahisar, a cewar ma’aikatar.

Ma’aikatar ta ce Turkiyya za ta ci gaba da yaƙinta da FETO da muƙarrabanta.

Ƙoƙarin juyin mulkin da aka samu galaba a kansa, inda aka kashe mutum 253 kuma aka raunata 2,734 , FETO ce ta kitsa shi tare da aiwatar da shi a ƙarƙashin shugabanta, Fetullah Gulen.