Shugaban Turkiyya Erdogan ya karbi sabon samfurin motar Togg T10F da aka ƙera a ƙasar

Shugabannin Togg sun miƙa motar lantarkin ga shugaban inda ya yi gwajin tuki da motar mai launin shuɗi, wadda aka liƙa mata tambarin shugaban ƙasa a wurin lambar motar.
13 Sep, 2025
Matar Shugaban Turkiyya ta yi kira kan samar da tsari ilimi mai daraja a duniya a taron Kiev

Emine Erdogan ta jaddada cewa ilimi shi ne babban makamin magance matsalolin duniya, tana mai bayani kan shirye-shiryen Turkiyya na ayyukan taimako da jinƙai.
12 Sep, 2025
Turkiyya ta yi tur da harin da Isra’ila ta kai kan tawagar Hamas a Qatar

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi kakkausan gargaɗi da yin tur da “manufofin Isra’ila na faɗaɗa mamaya.”
10 Sep, 2025
Mummunan harin da aka kai caji ofis a yammacin Turkiyya ya yi sanadin shahadar ‘yan sanda biyu

An kama wani matashi ɗan shekara 16 da ake zargi da kai harin bindiga a lardin Izmir na ƙasar Turkiyya, wanda kuma ya yi sanadin jikkata wasu ‘yan sanda biyu.
8 Sep, 2025

Sauyi mai kare yanayi na makamashi na ƙara inganci, amma zai iya gabatar da sabbin ƙalubale: Rahoto

Turkiyya ba za ta taɓa yin shiru game da zaluncin Netanyahu kan Falasɗinawa ba: Erdogan

Emine Erdogan ta yi kira ga ƙarfafa haɗin kan al’adu da muhalli a wajen taron SCO

Turkiyya za ta ƙaddamar da layin sadarwa na 5G nan da 2026

Turkiyya da Pakistan za su ci gaba da yaƙi da kisan ƙare-dangin da Isra’ila ke yi a Gaza: Erdogan
31 Aug, 2025
Shugaba Erdogan ya jinjina wa Jaruman Turkiyya a Ranar Nasara
Shugaba Erdogan a cikin saƙonsa na ranar Asabar, ya bayyana wannan rana a matsayin alamar imani mai ƙarfi na ‘yan ƙasar, ruhin jarumtaka, da kuma haɗin kai wajen yaƙi don ‘yanci da cin gashin kai.

30 Aug, 2025
Majalisar Dokokin Turkiyya ta yi kira kan a dakatar da Isra’ila daga MDD kan kisan ƙare-dangi a Gaza
Israila ta kashe kusan Falasɗinawa 63,000 a Gaza tun daga Oktoban 2023. Yaƙin ya lalata yankin wanda a halin yanzu yake fuskantar yunwa.

29 Aug, 2025
Kamfanin HAVELSAN na Turkiyya mai samar da jirage marasa matuƙa ya ƙulla yarjejeniya da Masar
HAVELSAN ya yi ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa tare da Hukumar Masana’antu ta Larabawa ta Masar (AOI) don samar da jirage marasa matuƙa ga Masar.

25 Aug, 2025
Shugaban leken asiri na Turkiyya Kalin ya haɗu da Haftar na Libya a Benghazi
Wata tawaga daga Ma’aikatar Tsaron Ƙasa ta Turkiyya, ƙarƙashin jagorancin Manjo Janar Ilkay Altindag, ta kai ziyara ga Haftar, mataimakin kwamandan Rundunar Sojan Ƙasa ta Libya, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana a dandalin sada zumunta na NSosyal.

25 Aug, 2025
Wasiƙar da Mai Ɗakin shugaban Turkiyya ta aike wa Melania Trump kan Gaza ta ja hankalin duniya
A wasiƙar tata, Emine Erdogan ta buƙaci Melania Trump ta nuna jinƙai ga yaran Gaza kamar yadda take nunawa na Ukraine.

24 Aug, 2025
Matar Shugaban Turkiyya ta aika wasiƙa ga Melania Trump, ta buƙaci ta nuna goyon baya ga yaran Gaza
A cikin wasikar da ta aika wa Uwargidan Shugaban Amurka, Emine Erdoğan ta jaddada cewa ‘yancin kowane yaro na girma cikin aminci haƙƙi ne na duniya baki ɗaya, dole ne a kare shi ba tare da la’akari da wurin zama, jinsi ko addini ba.

23 Aug, 2025
Zeytin: Jaririn goggon birin da aka kubutar a filin jirgin saman Istanbul na shirin komawa Nijeriya
Jaririn goggon birin da aka yi fasa-kwaurinsa aka kuma gano shi a filin jirgin sama na Istanbul, na shirin komawa gida Nijeriya, bayan ba shi kulawa a Istanbul ya kuma murmure, kamar yadda hukumomin Turkiyya suka bayyana.

23 Aug, 2025
Turkiya ta yi nasarar gwajin Simsek, wani jirgi maras matuƙi mai matuƙar gudu
Jirgin wanda ake harbawa kamar roka, ya tashi daga ƙasa a karon farko, kuma za a iya amfani da shi a matsayin jirgi domin kai hari da kuma wurin kai harin ƙunar baƙin-wake.

22 Aug, 2025
Turkiyya na binciken Google kan tilasta wa manhajoji amfani da tsarin biyan kuɗi na Play Store kaɗai
Hukumomi a Turkiyya za su binciki Google kan tilasta wa manhajoji amfani da tsarinsa na biyan kuɗi da kuma hana mutane amfani da wasu hanyoyin biyan kuɗi na daban.

21 Aug, 2025
Ziyarar Erdogan zuwa Somalia a shekarar 2011 ce ta sauya tarihin ƙasar: Ministan Somalia
Ziyayar Shugaba Recep Tayyip Erdogan mai cike da tarihi zuwa Somalia a shekarar 2011, yayin da yake Firaminista, ta yi tasiri a zukatan mutane.
