Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin soji kan Oman idan ta tsoma baki cikin tattaunawar Amurka da Iran, yayin da yake cewa Washington tana tuntuɓar jami’ai daga Rundunar Kare Juyin Juya Halin Iran (IRGC) kai-tsaye.
“Idan Oman ta kawo cikas, za mu far musu da harin bam,” kamar yadda Trump ya shaida wa tashar Fox News ranar Litinin a lokacin da aka tambaye shi game da rawar da Oman ke takawa a tattaunawar Iran da Mashigar Hormuz.
Iran ta bayyana ranar Asabar cewa ta cim ma yarjejeniya da Oman kan wata taswirar hanyar jiragen ruwa ta Mashigar Hormuz, bayan makonni suna tattaunawa.
Da ya koma kan Iran, Trump ya ce ya kamata Tehran ta ɗaga “farar tutar miƙa-wuya,” yana mai ƙarawa da cewa: “Sun ƙware a karta, amma suna ta mutuwa.”
Ya kuma tabbatar da cewa Washington na da hanyar bayan fage ta magana da IRGC.
“Muna da wata hanya ta bayan fage [ta magana] da IRGC. Muna magana kai-tsaye da jami’an IRGC a Iran,” in ji Trump.
Hare-haren Isra’ila kan Gaza
Game da Gaza, Donald Trump ya ce: “‘bai kamata Isra’ila ta yi ta kai hari a Gaza ba. Tuni Hamas sun yarda su ajiye makamansu.”
Trump ya kuma bayyana cewa Amurka na da wata hanya ta daban ta tattaunawa da Hamas.
“Muna da wata hanya ta daban ta magana da Hamas, kuma daga ƙarshe dai za su ajiye bindigoginsu,” in ji shi.
Kalaman na zuwa ne yayin da Washington ke matsawa da ƙoƙarin aiwatar da shirin zaman lafiyar Trump na Gaza, wanda ya haɗa da ajiye makaman Hamas da kuma janyewar sojin Isra’ila daga yankin.
Da aka tambaye shi game da siyasar Isra’ila, Trump ya ce ya yi imanin cewa abu da “ya fi dacewa” shi ne shi ya ƙaurace tsoma baki a zaɓen ƙasar, yayin da yake nuna yiwuwar nuna zaɓinsa na ɗantakaran da ya kamata a zaɓa.
“Ina tunanin abu ne da ya fi dacewa gare ni ne na ƙaurace wa tsoma baki a zaɓen Isra’ila, amma zan iya nuna wanda nake son a zaɓa,” in ji shi.















