Sojojin Sudan sun ƙwace iko da wani muhimmin birni a kusa da iyakar Habasha bayan arangama da RSF

Sojojin Sudan ɗin sun ce sun jawo babbar asara ga rundunar ‘yantawayen inda suka yi asarar rayuka da kuma ta kayan aiki.

Newstimehub

Newstimehub

16 May, 2026

1777741669938 e0aai6 faf692e1b72be20253da03e27c43671d0e51ffc0ab614ec7a4d9193363215906

Sojojin Sudan a ranar Jumma’a sun sanar da cewa rundunarsu ta karɓi iko da yankin Khor Hassan a Jihar Blue Nile daga Rundunar Rapid Support Forces RSF.

A cikin wata sanarwa, sojojin sun tabbatar da “‘yanta Khor Hassan a Jihar Blue Nile bayan yakin da suka yi da dakarun ‘yantawaye na RSF da abokan su na Sudan People’s Liberation Movement-North (SPLM-N).”

Sanarwar ta ce sojojin sun jawo babbar asara ga rundunar ‘yantawaye inda suka yi asarar rayuka da kuma asarar kayan aiki.

Yankin Khor Hassan na da muhimmanci sakamakon wurin ya take a ƙasar domin yana ƙara ba sojoji kusanci wajen sake samun iko da garin Kurmuk, wanda ke kan iyakar Habasha.

A ‘yan makonnin da suka gabata, Jihar Blue Nile ta sha fama da ƙaruwa a rikice-rikice wanda ya sa dubban mutane suka bar gidajensu daga yankuna da birane da dama a cikin jihar.

Sudan ta fuskanci ɗaya daga cikin mafi munin rikice-rikicen jin kai a duniya tun bayan da yaƙi ya ɓarke a Afrilun 2023 tsakanin sojoji da RSF kan sabani game da yadda za a haɗa wannan rundunar ta sa kai cikin sojojin ƙasa. Wannan rikicin ya janyo yunwa, ya kashe dubban mutane, kuma ya tilasta miliyoyin mutane yin gudun hijira.