Sojojin Burkina Faso a ranar Laraba sun ce sun daƙile hare-haren da ƙungiyoyin ‘yanta’adda suka kai wasu sansanonin soji a ranar 30 ga Yuni, inda aka kashe fiye da mahara 400.
Sojojin sun daƙile harin ne bayan samun taimako daga jiragen sama.
A cikin wata sanarwa da Hedkwatar Sojin Burkina Faso ta fitar ranar Laraba da daddare, ta ce ‘yanta’addan sun kai hare-hare kan sansanonin soji da kuma jami’an sa-kai don kare ƙasa a ƙauyukan Gayeri da ke yankin Sirba, da Solhan da Sebba a yankin Liptako.
A cewar rundunar, sojojin ƙasa, tare da goyon bayan jiragen sama, sun mayar da martani nan-take ga hare-haren.
Sun ce “hare-hare ta sama da ta ƙasa sun yi sanadin kashe ‘yanta’adda fiye da 400” da ba su damar ƙwato kayayyakin yaƙi masu yawa, ciki har da babura fiye da 250, makamai 353 na nau’o’i daban-daban, harsasai da kayayyakin sadarwa.
Sojojin sun kuma bayar da rahoton mutuwar jami’ansu guda uku yayin fafatawar, ciki har da biyu a Solhan da ɗaya a Gayeri.
“Ayyukan tsaro na ci gaba kuma suna ƙaruwa domin bin diddigin waɗanda suka gudu da tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan ƙasa,” in ji rundunar.
Ta roƙi mazauna su haɗa gwiwa da jami’an tsaro, su bi umarnin tsaro, su kuma ba da rahoton mutanen da ake da shakku a kansu.
Sanarwar ta alaƙanta hare-haren da yanke hulɗar diflomasiyya da Burkina Faso ta sanar da Faransa inda aka kai harin kwana guda bayan sanarwar.
Burkina Faso ta kuma zargi ƙasar Faransa da bayar da goyon baya ga ƙungiyoyin ‘yanbindigar.















