Sojin Sudan ta yarda da ‘zaman lafiya ta gaskiya’ ba tare da RSF ta ƙwace iko ba, in ji Janar Burhan

Babban hafsan sojin Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya ce dole a fara zaman lafiyar da ajiye makaman rundunar RSF da kuma dawo da tsaro da rayuwar yau da kullum.

Newstimehub

Newstimehub

15 Aug, 2026

86c44a20 62aa 4161 ab70 a3f26900efc7 1786786479178

Shugaban gwammatin riƙon ƙwarya na Sudan Abdel Fattah al-Burhan ya ce rundunar sojin ƙasar ta jajirce wajen cin galaba a kan rundunar RSF, amma ya tabbatar da cewa ƙofarta abuɗe take ga abin da ya kira shirin zaman lafiya “na gaskiya,” kamar yadda kamfanin dillancin labaran ƙasar SUNA ya ruwaito ranar Asabar.

A wani jawabi na cikan shekara 72 da kafa rundunar sojin ƙasar (SAF) ranar Jumma’a, Burhan ya bayyana cewa jajircewar sojin wajen yaƙar tare da cin galaba a kan RSF “ba ya nufin kawar da kai ga ko wane shiri na gaskiya na zaman lafiya,” in ji kamfanin dillancin labaran ƙasar SUNA.

“Ƙoƙarinmu wajen samun wannan bai tsaya ba tun watannin farko na tawayen, amma ba za mu lamunci zaman lafiyar da ba cikakkiya ba ce ko kuma wata zaman lafiyar da za ta mayar da masu aikata laifuka da masu kisan kai (shugaban RSF Mohamed Hamdan​​​​​​​) mayaƙan Dagalo da masu mara msu baya, kan mulki ko kuma kasancewa ciki masu mulki,” in ji shi.

“Matsayarmu a bayyane take tun watan Mayun shekarar 2023: Hanyar zuwan zaman lafiya za ta fara ne da ajiye makaman waɗannan mayaƙan da kuma taruwarsu a wuraren da aka tsara, da kuma ‘yanƙasa su fara komawa wurarensu kuma rayuwa ta koma yadda aka saba da ayyuka da tsaro da kariya da kuma sa-ido,” in ji Burhan.

“Bayan wannan, yanayin mayaƙa da ba masu aikata laifuka ba ne za a iya sake duba lamarinsu,” in ji shi.

Tattaunawar ‘yan Sudan kawai

A fannin siyasa, Burhan ya ce ya fara tattaunawa da ƙungiyoyi na ƙasa da ɓangarori da suka “goyi bayan ƙasar Sudan da haɗin kanta da hukumominta” domin saka su cikin ƙoƙarin cika hukumomin ƙasa ciki har da majalisar dokoki.

Ya bayyana samar da majalisar dokoki a matsayin “wata buƙata ta tsarin mulki.”

Burhan ya kuma bayyana abin da ya kira “zahirin na tsauri na siyasar ” ƙasar, inda wasu maza da mata ‘yan Sudan suka kafa wani tsari bisa “imani mai ƙarfi cewa cin galaba a kan wannan matsalar za iya yiwuwa ne kawai ta hanyar tattaunawa ta ‘yan Sudan kaɗai.”

Ya ce irin wannan tattaunawar ya kamarta ya samo asali ne “daga cikin gida kuma ya haɗa da dukkan ɓangarorin siyasa da na zamantakewa ,” yayin da yake saka “wahalar ‘yanƙasar da ‘yancinsu na zaman lafiya a gaba-gaba a burinsa.”

Sudan ta faɗa cikin rikici tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF tun watan Afrilun shekarar 2023, wani yaƙin da ya kashe gomman dubban mutane da kuma raba kusan mutum miliyan 13 da gidajensu, in ji kiyasin Majalisar Ɗinkin Duniya da na ƙasashen duniya.